5.53 Ni Chadi Zan Tafi
Wannan wasa ma ta tashe ne da yara maza ke gudanarwa. Adadin masu gduanarwar na kaiwa bakwai zuwa sama da haka. Sannan ana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi. Yana kuma cikin rukunin wasanni da ke tafiya da waƙa. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashe, akan gudanar da shi ne da dare, bayan an sha ruwa.
5.53.1 Kayan Aiki
i. Tsohuwar jaka ko leda
ii. Kayan sawa ko wasu tsommokara
iii. Kayan dattawa da suka haɗa da babbar riga da rawani da hula, amma tsofi
iv. Kayan mata da suka haɗa da zane da kallabi da sauransu, su ma tsofi
5.53.2 Yadda Ake Wasa
Ɗaya daga cikin yara zai yi shigar maza dattawa, ɗaya kuwa ya yi shigar mata. Wato ta hanyar amfani da kayan aiki da aka lissafa a sama. Kowannensu zai riƙe faggon kaya, ko dai a cikin tsohuwar jaka ko wata leda. Za kuma a samu wasu yaran guda biyu ko uku waɗanda ba su kai waɗannan biyu girma ba, su kasance a gaba. Wato dai kamar yadda iyaye ke sa ‘ya’yansu gaba yayin tafiya. Sauran ‘yan wasa kuwa za su biyo su a baya.
Yayin da aka je wurin da za a gabatar da tashe, wanda ya yi shigar dattawa zai riƙa ba da waƙa, sauran yara kuwa na amsawa. Ga yadda waƙar take:
Bayarwa: Kai ni Chadi zan tafi,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Ga mata ga ‘ya’ya,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Mata har guda huɗu,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: ‘ya’ya goma sha tara,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Ga shi ko babu ko kwabo,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Ga shi ko ba hatsin tuwo,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Kai ni Chadi zan tafi,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
Bayarwa: Ku bar ni fa Chadi zan tafi,
Amshi: Fatarar bana ba kai kaɗai ba ne.
5.53.3 Tsokaci
Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Wasan na ɗauke da hoton wani lamari da kan faru a ɗaiɗaikun lokutan da mai gida ya shiga cikin wani hali. Wannan lamari kuwa shi ne hijira ko ci-rani. Aure ke nan, ka gagari manya yara na ganin damarka.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.