Ticker

6/recent/ticker-posts

Danda Dokin Kara

5.47 Danda Dokin Kara

Wannan wasan maza ne da ke cikin rukunin wasannin tashe. Yana tafiya da waƙa. Sannan yana da buƙatar kayan aiki domin gudanarwa. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa.

5.47.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Masu wasa sukan bi shaguna da wuraren da mutane ke taruwa da kuma gidaje domin gudanar da wannan wasan tashe.

ii. An fi gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Wato dai saɓanin mafi yawan wasannin tashe da ake gudanarwa da dare bayan an sha ruwa.

5.47.2 Kayan Aiki

i. Karan dawa mai ƙarfi da kauri

ii. Ƙyallaye

iii. Babbar riga/malum-malum

iv. Rawani

v. Igiya (a matsayin linzami)

5.47.3 Yadda Ake Wasa

Yara za su samu karan dawa mai ƙarfi da kauri su ɗaɗɗaura masa ƙyallaye a matsayin doki. Za su yi haka cikin kwaikwayon yadda ake kwalliyar doki. Ɗaya daga cikin yaran kuma zai yi shiga irin ta sarauta. Wato zai sanya babbar riga ya sha rawani, sannan ya hau wannan dokin kara.

Yayin da aka iso wurin tashe yaron da ke bisa dokin zai riƙa waƙa, sauran yara kuma na amsawa. Waƙar kuwa ita ce:

Bayarwa: Assalamu alaikum kun yi baƙo,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Masu gidan nan kun yi baƙo,

Amshi: Ga danda dokin kara.

 

Bayarwa: Sai ku ban kaji bakwai daƙwale,

Amshi: Ga danda dokin kara.

Bayarwa: Da tuwon shinkafa da miya ja,

Amshi: Ga danda dokin kara.


Bayarwa: Sai ku ban soyen nama na rago,

Amshi: Ga danda dokin kara. 

5.47.4 Tsokaci

Wannan wasa kwaikwayo ne ga shigar sarauta da kuma al’adar Bahaushe na yi wa doki kwalliya. Sai dai an shirya shi ne kawai domin nishaɗantarwa. Idan ba haka ba, ina aka taɓa ganin sarki da kwaɗayi?

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments