Ticker

6/recent/ticker-posts

Alhajin Kauye

5.48 Alhajin Ƙauye

Wannan wasa yana ɗaya daga cikin wasannin tashe na maza. Yana tafiya da waƙa, sannan akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Kimanin mutane huɗu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Kamar sauran wasannin yara maza, masu wasa sukan bi gida-gida da kuma wurin zaman jama’a ko sana’arsu a dandali domin gudanar da shi.

5.48.1 Kayan Aiki

i. Kayan dattawa, kamar babbar riga da rawani da hula

ii. Auduga (domin yin gemu da saje)

iii. Sanda

iv. Tsohuwar jakar sanya tufafi ko wata babbar leda

v. Tsummokara

5.48.2 Yadda Ake Wasa

Za a yi amfani da abubuwan da aka lissafa ƙarƙashin 5.48.1 domin a shirya ɗaya daga cikin ‘yan wasa cikin shigar tsofi. Wanda aka yi wa wannan shiga akan kira shi da suna ‘Alhajin Ƙauye.’ Alhajin ƙauye zai riƙe sanda sannan ya ratayo jaka ko ledar da aka cusa wa tsummokara. Zai shige gaba yana dogara sandansa yana tafiya a sussunkuye. Sauran yara kuwa za su bi shi a baya.

Yayin da suka isa wurin tashe, za su fara waƙa kamar haka:

Bayarwa: Alhajin ƙauye,

Amshi: Ya yi azumi zai je shi gida.

Bayarwa: Ba kuɗin mota,

Amshi: Ya yi azumi zai je shi gida.

Bayarwa: Ba kuɗin taya,

Amshi: Ya yi azumi zai je shi gida.

5.48.3 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana nuni ga wata al’ada ta Hausawa, wato taimakon marasa ƙarfi da kuma matafiya. Tun asali dai Bahaushe mutum ne mai karrama baƙi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments