Ticker

6/recent/ticker-posts

Afajana

5.46 Afajana 

Wannan wasa ne na yara maza. Yawanci adadin masu gudanar da wannan wasa kan kai goma zuwa sama da haka. An fi gudanar da shi da hantsi ko da yamma. Sai dai a wasu lokuta akan gudanar da shi da dare, yayin da akwai farin wata sosai. Yana cikin rukunin wasannin yara maza da ba sa tafiya da waƙa. Sannan akan gudanar da wannan wasa a dandali, ko ko a keɓaɓɓen wurin da ba yawan wucewar jama’a. Akan yi amfani da kayan wasa, wanda kuwa shi ne riguna.

5.46.1 Yadda Ake Wasa

Wannan wasa yana kama da wasan Tarkon Horon Wawa. Sai dai tsarinsu ya bambanta. A wasan afajana, yara sukan tuɓe rigunansu, sannan su tara su wuri guda. Daga nan za su koma gefe guda. Sai kuma mutum guda da bai aje rigarsa ba ya matso kusa da tarin rugunan da ke ajiye. Wannan shi ake kira sarki a cikin wasan. Sannan wani yaron daban zai tsara ta ɗaya ɓangaren kayan. Shi kuma ana kiransa turke.

Sarki da turke za su riƙe riga guda, wato kowa ya riƙe ƙarshenta ta ɓari guda. Za su tsaya daidai wurin da kayan suke, yadda babu mai ida ɗaukar rigarsa sai ya miƙa hannu ta ƙasar wannan riga da sarki da kuma turke ke riƙe da ita.

Daga nan sauran yara za su fara dabaru iri-iri domin su ɗauki rigunansu. Za su riƙa jan hankalin sarki tare da amfani da hanyoyin iri-iri. Ana so a ɗauki rigar ne ba tare da sarki ya taɓa ko ya kama yaro ba. Da zarar sarki ya taɓa wani, to wanda aka taɓa shi ne zai zama sarki. Yayin da wani yaro ya ɗauki rigarsa ba tare da sarki ya taɓa shi ba, zai nannaɗe rigar sannan ya fara dukan sarki da ita. Ta haka sauran yara za susa musu ɗauki rigunansu. Su ma kuwa haka za su ci gaba da bugun sarki. Sarki kuwa zai yi ta faman taɓa ɗaya daga cikinsu.

Haka dai za a yi ta dukan sarki har sai ya taɓa ɗaya daga cikin yaran. Wani lokaci kuma wani yaro zai iya cewa ya karɓa masa. Saboda haka shi yaron ne zai zama sarki. Yayin da ake faman ɗaukar riga kuwa. Sarki zai iya cewa ya ba da sadaka, saboda haka kowa ya ɗauki riga ba tare da an taɓa shi ba. Sai bayan sun gama ɗauka ne kuma zai yi faman bin su da gudu domin ya taɓa ɗayansu.

5.46.2 Tsokaci

Haƙiƙa wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da su jarumta da juriya da kuma dabarun kare kai. Rago ko malalaci ba zai iya wannan wasa ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments