Ticker

6/recent/ticker-posts

Motar Kara

5.44. Motar Kara

Wannan ma wasa ne na yara maza. Babu wani adadi na yaran da ke haɗuwa domin gudanar da wannan wasa. A maimakon haka, yaro guda na iya gudanar da wannan wasa. Sannan yara da dama na iya haɗuwa wuri ɗaya domin gudanar da wasan motar kara. Akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.44.1Wuri Da Lokacin Wasa

i. Babu wani takamaiman wuri da aka fi gudanar da wannan wasa. Yakan kasance a gida ko a dandali ko bisa titi da makamantansu.

ii. An fi gudanar da wannan wasa da hantsi da kuma yamma. Ba a faye yin sa da dare ba. Sannan wannan wasa yana da lokacin da ake yin sa cikin shekara. Wato bayan an gama girbe amfanin gona.

5.44.2Kayan Aiki

i. Sillen karan dawa

ii. Igiya ko zare

iii. Mataccen takalmi silifa ko marfin murtan man shafawa ko matacciyar ƙwarya

iv. Gajeruwar kara

v. Reza ko wani abu mai kaifi

5.44.3 Yadda Ake Wasa

Wannan wasan hawa biyu ne. Hawa na farko shi ne haɗa ko ƙera motar karan kanta. Hawa na biyu kuma shi ne wasa da motocin karan bayan an kamala su. Yayin haɗa motar kara, yara za su nemo sillayen kara. Adadin sillayen karan za su kasance daidai da girman motar da aka ƙudurta ƙerawa. Za a ɓare waɗannan sillayen kara tas.Sannan a hau haɗa mota.

Motar da za a haɗa kwaikwayo ce na ɗaya daga cikin irin motocin da yara suka saba gani. Ko dai ƙaramar mota ko babba. Ko rufaffiya ko kuma mai buɗaɗɗen baya wato bodi. Yara sukan yi amfani da ɓawon sillen da suka ɓare wurin haɗa sille da sille wuri ɗaya. Wato za su cusa ɓawon sai ya ɓula ɓararren sillen ya wuce ya ɓula na gaba da shi. A haka za su haɗe wuri ɗaya ɗaram. Akan yi amfani da reza ko wani abu mai kaifi wurin yanka ɓararrun sillayen karan zuwa daidai tsawon da ake buƙata. Kyawun motar yaro ta danganta da ƙwarewarsa da kuma lokacin da ya ɓata wurin haɗa ta.

Bayan an kamala mota sai maganar tayu. A nan yara na amfani da marafan murtan man shafuwa ko fashasshiyar ƙwarya ko kuma tsohon takalmi silifa. Idan matacciyar ƙwarya ce ko kuma takalmi, za a yanka shi rawul, wato zagaye, tamkar dai taya. Sannan sai a nemi ƙusa a huda tsakiyar. Yawanci akan sanya ƙusar a wuta kafin a kai ga hudawa gudun kada abin ya fashe ko ya ƙi huduwa mai kyau. Bayan tayu sun haɗu, za a sanya su wurin da suka dace a jikin motar. Wata motar za ta kasance mai taya huɗu, wata shida wata sama da haka. Wannan ya danganta da girman motar da tsarinta.

Bayan an kamala sanya tayu a mota, sai kuma a nemi igiya ko zare a ɗaura a gabanta. Wannan shi ne tamkar matuƙi. Da shi ne yara ke jan motar zuwa wurin da suke buƙata. Masu mota sukan iya fita wasan tserel ɗin mota bisa tituna. Wani lokaci kuma yaro na tafiya da motarsa yayin da aka aike shi siyo kayan miya ko wani abu mai kama da wannan. Nan za a ga yaro na faman gudu zuwa wurin aika tare da mota, har diri yake mata da baki.

5.44.4Tsokaci

Wannan wasa ne da ke samar da nishaɗi ga yara. Sannan yana wasa musu ƙwaƙwalwa ta hanyar ba su gogewa a ɓangaren fikirar ƙere-ƙere.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments