Ticker

6/recent/ticker-posts

Gwanjo-Gwanjo

5.43 Gwanjo-Gwanjo

Wannan ma wasan yara maza ne. Yara misalin goma zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. Wasa ne da ke buƙatar hanzari da zafin nama. Sannan yana cikin jerin wasannin Bahaushe da ke da hukunci. Wannan wasa ba ya tafiya da waƙa. A maimakon haka, yara sukan yi shewa ne. Sai dai akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.43.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Ana gudanar da wannan wasa a dandali.

ii. Akan yi wasan da yamma ko da dare lokacin da farin wata ke da haske sosai.

5.43.2 Kayan Aiki

i. Riguna

ii. Bishiya ko garu ko wani wurin sha.

5.43.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tuɓe rigunansu. Sai a haɗa rigunan wuri ɗaya, ya cakuɗa su. Daga nan mutum ɗaya zai riƙe rigunan ya tukuikuya su wuri ɗaya, su kasance a mulmule. Sai kuma ya jefa su zuwa sama. Yara za su ɗau shewa gaba ɗaya:

“Gwanjo-gwanjo!”

Tun rigunan suna sama yara za su daka wawa. Kowa zai yi ƙoƙari tsaƙulo rigarsa. Da zarar yaro ya ɗauki rigarsa, zai yi ƙoƙarin nannaɗa ta yadda za ta zama mai daɗin duka. Sannan zai ja gefe guda ya tsaya. Da zarar kowa ya gama ɗaukar rigarsa ya rage saura mutum guda, za a rufe wannan yaro da bugu. Shi kuwa zai yi ta ƙoƙarin gudu zuwa wurin sha. Ba za a rabu da shi ba har sai ya sha.

5.43.4 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana koyar da hanzari da zafin nama da kuma jarumta.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments