Ticker

6/recent/ticker-posts

Tarkon Horon Wawa

5.42 Tarkon Horon Wawa

Wannan ma wasa ne na yara maza. Kimanin mutane goma ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Yayin da yara ke da yawa, wasan ya fi daɗi. Wasa ne da ba ya tafiya da waƙa. Amma akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.42.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Ana gudanar da wannan wasa a dandali.

ii. Akan yi wasan da yamma ko da dare lokacin da farin wata ke da haske sosai.

5.42.2 Kayan Aiki

i. Riguna

ii. Igiya ko tsumma

5.42.3 Yadda Ake Wasa

Akan samu yaro ɗaya a ɗaura masa igiya ko wani tsumma a kunkumi. Wani yaron daban zai kasance a bayan wadda aka ɗaura wa igiya, sannan ya kama igiyar ta baya. Sai kuma dukkanin yara su tuɓe rigunansu. Za a haɗa rigunan wuri guda a cakuɗa su, sannan a ajiye su gaban wanda aka ɗaura wa igiya a kunkumi. Shi kuwa zai tuɓe rigarsa ya nannaɗe ta yadda za ta yi daɗin duka.

Da zarar an kamala shiri. Yara za su riƙa zuwa ɗaya bayan ɗaya suna ɗaukar rigunansu. Wanda ke riƙe da igiya zai riƙa ƙoƙarin jan wanda aka ɗaura wa igiya a baya. Shi kuwa wanda aka ɗaura wa igiya zai riƙa dukan duk wanda ya zo ɗaukar rigarsa ta amfani da rigar da ya nannaɗa ya riƙe a hannu. Duk wanda ya kasa ɗaukar rigarsa da wuri, to kuwa zai sha bugu, har sai ya ɗauka. Sassaucin kawai da ake samu shi ne kasancewar ana ta ƙoƙarin jan mai dukan zuwa baya.

5.42.4 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki. Baya ga haka, yana koyar da yara jarumta da saurin hannu, wato gaggawa wurin aikata aiki.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments