Ticker

6/recent/ticker-posts

Dirke-Dirke

5.41 Dirƙe-Dirƙe

Wannan ma wasan yara maza ne. Yana ɗaya daga cikin jerin wasannin ƙiriniya. Yara da dama sukan yi wannan wasa ne ba tare da sanin iyayensu ba. Wasu yaran sukan sha zagi ko ma duka yayin da aka san sun je wannan wasa a gida. Wasa ne da ba ya ɗauke da waƙa. Sannan ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.41.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Ana gudanar da wannan wasa ne a rafi ko kogi wanda ruwansa ya janye, wanda kuma ke da yashi ciki.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da dare.

5.41.2 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tafi wurin rafi ko kogin da ruwa ya janye wanda kuma ke da yashi. Daga nan za su samu wani wuri mai ɗan tsawo (daidai da yadda marasa tsoron cikinsu za su iya dirgawa). A wannan wuri ne za su riƙa tsayawa sannan su daka tsalle su tuma cikin yashin. Idan wurin dirgawar yana da faɗi, yara biyu ko sama da haka na riƙe hannun juna sannan su dirga tare.

5.41.3 Tsokaci

Wannan na ɗaya daga cikin wasannin yara maza da suke da ɗunbin kasada tattare da su. Sau da dama yara sukan fasa bakinsu ko su gurɗe (samu targaɗe) ko ma su karye. Wasa ne da ke sanya jarumta da rashin tsoro ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jini.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments