Ticker

6/recent/ticker-posts

Baba Mai Gadi

5.36 Baba Mai Gadi

Wannan wasa ne na yara maza. Yana cikin rukunin wasannin tashe. Ana buƙatar kayan aiki kafin yayin gudanar da shi. Sannan wasa ne da ke tafiya da waƙa. Kimanin yara huɗu zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa. An fi gudanar da shi lokacin da ido ke gani (saɓanin lokacin gudanar da tashe na asali, wato dare). Amma akan yi shi da dare, bayan an sha ruwa.

5.36.1 Kayan Aiki

i. Kayan maza da suka haɗa da babbar riga da hula da makamantansu

ii. Auduga (a matsayin gemu)

iii. Wani abu mai danƙo da za a iya laƙa auduga da shi

iv. Sanda

5.36.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa sukan zaɓi ɗaya daga cikinsu ya zama Baba Mai Gadi. Zai yi shigar tsofi ta hanyar sanya babbar riga da hula da kuma rawani. Za kuma a masa farin gemu da saje na auduga. Sannan zai nemi sanda ya riƙe.

Yayin da ake je wurin tashe, Baba Mai Gadi zai wuce gaba. Sauran yara za su riƙa waƙa tare da tafi. Shi kuwa zai fara tiƙar rawa tare da dogara ɗan sandarsa, yayin da kuma yake amsa waƙar. Ga yadda waƙar ta ke:

Yara: Baba Mai Gadi rawar cokon za ka yi?

Baba Mai Gadi: A’a yaran zamani,

Kar ku sa ni in haukace,

Ni masallaci za ni je.

Haka za su ci gaba da wannan waƙar, Baba Mai Gadi kuwa yana ta taka rawa tsofai-tsofai.

5.36.3 Tsokaci

An gina wannan wasa kan nishaɗantarwa. Sannan kamar wasannin tashe da yawa, yana nuni ga bauta cikin watan azumi. Duk da dai Baba Mai Gadi yana ta tiƙar rawarsa, zuwa masallaci ne a cikin zuciyarsa.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments