5.37 Bindiga
Wannan nau’in wasan yara ne da ake yayinsa a shekara-shekara. Yara sukan yi wannan wasa a matsayin ɗaiɗaiku ko kuma ƙungiya-ƙungiya. Ma’ana dai, yaro ɗaya ma zai iya wannan wasa a karan kansa. Amma lokuta da dama yara kan haɗu ne domin ƙera bindigogin wasan.
5.37.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Wannan wasa ba ya da taƙamaiman wurin da ake gudanar da shi. Akan yi shi a dandali, ko bayan gari wani lokaci ma har da cikin gidaje.
ii. Ba a ware wani lokaci na musamman ba da ake gudanar da wannan wasa. Akan yi wasan da hantsi ko da yamma ko ma da dare.
5.37.2 Kayan Aiki
i. Katako ko falanki ko filawud
ii. Robar tib ta mashin ko ta keke
iii. Ashana
iv. Ƙarfen wayar gareren keke ko ta mashin
v. Zarto ko seya ko wani abin yanka makamancin wannan
vi. Siririn ƙarfe mai kwararo a tsakiya
5.37.3 Yadda Ake Wasa
Yara kan sami katako ko filawud ko falanki, sai su yanke shi da zarto ko wani abin yanka. Za a zamar da shi mai siffar ‘L.’ Sai kuma a samo siririn ƙarfe mai kwaroro a tsakiya. Za a lanƙwasa ƙarshen bakin wannan ƙarfe, a dandaƙe da dutse yadda wani abu ba zai iya zubowa ta wurin ba yayin da aka ɗura ta ɗaya bakin. Daga nan za a yanka wannan ƙarfe daidai tsawon da za a iya ɗorawa bisa wannan katako da aka yanka zuwa ‘L.’ Sai a ɗora shi bisa wannan ƙaramin katako a samu robar tib ta mashin ko keke a ɗaure shi tam yadda ba zai riƙa motsi ba.
A ɗaya ɓangaren kuma, za a samu wayar gareren mashin ko keke a yanke ta daidai tsawon da zai iya kaiwa ƙarshen kwararon siririn ƙarfe da aka ɗaure jikin katako. Ƙarshen wayar za a lanƙwasa shi ya zama mai gewaye. Cikin wannan gewaye za a sanya roba ta tib ɗin mashin ko mota, gajeruwa. Sannan za a ɗaure wannan roba a jikin katakon da aka yi wa L. Abin zai kasance yadda sai an ja wannan roba da ƙarfi kafin wayar ta shiga cikin kwararon ƙarfen da ke ɗaure jikin wannan L. Yayin da aka sake shi a ciki, ƙarshen wayar zai je ya doki ƙarshen wannan ƙarfe da ƙarfin gaske.
Yayin da wannan ya kammala, to an samu bindiga. Daga nan za a riƙa daka kan ashana. Sai a zuba garin cikin wannan kwaroro. Sai kuma a jawo wannan wayar gareren keke ko ta mashin a lojana shi a bakin kororon. Wannan shi ake kira da ɗani. Yayin da duk aka matsa robar da aka ɗaure wayar da ita, to ƙarshen wayar zai je ya doki garin ashanar da ke cikin kororon. Hakan zai ba da wata ƙara mai ƙarfi, daidai da yawan garin ashanar. Wani lokaci har wuta ke tashi a bakin kororon.
Akan yi rashin sa’a ta toye. Wato ta ba da wata ƙara ba mai ƙarfi ba, tare da hayaƙi. Yayin da haka ta faru, mai bindiga zai yi saurin hura cikin kororon sai kuma ya sake ɗani. Yayin da ya yi bugu na biyu, za a iya dace ta tashi. Wani rashin sa’a da ake samu shi ne bindigar ta yi wa mai bugawa feshi. Hakan na faruwa yayin da wannan garin ashana ya fantsama zuwa hannun mai bugawa. Hakan na wanzar da raɗaɗi mai tsanani ga hannun nasa. Sannan garin ashanar kan nitse cikin fatar hannun yadda sai an yi kwanaki ba su fita ba.
Wani lokaci akan iya haɗa bindiga mai tashi biyu, ko dai domin gwaninta da sabo ko kuma domin sa’a. Waɗanda bindigarsu ke tashi biyu sukan yi gadara da taƙama. Yayin da yara suka haɗa bindigogi, to iyayensu mata sai dai su yi ta kaffa-kaffa da ashanunsu. Domin kuwa ko dai yaran su riƙa sunkutar fankon gaba ɗaya, ko kuma su riƙa ɗauki ɗaɗɗaya ga ‘ya’yan ashanar.
Yara masu tsokala da jan faɗa kan laɓe hanyar da ake wucewa, yayin da tsoho ko tsohuwa (musamman kakan ɗaya daga ciki) ta zo wucewa, sukan buga wannan bindiga tare da tserewa yayin bayan sun firgita wadda suka buga wa. Wani lokaci kuwa a ‘yan mata suke yi wa wannan tsiya. A wasu lokutan irin waɗannan yara sukan sha duka idan sun kamu.
5.37.4 Tsokaci
Haƙiƙa wasan bindiga ya kasance mai jan ra’ayin yara matuƙa. Sai dai ba kowane yaro ba ne ake bari ya yi wannan wasa a gidansu. Musamman kasancewar yadda wasan ke tattare da ƙiriniya da kuma ta’adi.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.