Ticker

6/recent/ticker-posts

‘Yar Dille

5.35 ‘Yar Ɗille

Wannan wasa ne na yara maza. An fi gudanar da wannan wasa da damina lokacin da ƙasa take da damshi. Yara biyu ma za su iya wannan wasa a tsakaninsu. Sai dai wasan ya fi daɗi idan an samu kimanin yara uku zuwa sama da hakan (yawansu ba a so ya wuce biyar).

5.35.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Ana gudanar da wannan wasa a cikin gida, musamman gindin bishiya. Sannan akan gudanar da wasan a ƙofar gida ko dai wani wuri da ake samun taron yara.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma.

5.35.2 Kayan Aiki

i. Ƙaramin dutse (tsakuwa) ko ƙwallon aduwa ko wani abu makamancin wannan

ii. Tsinke mai ɗan kauri

5.35.3 Yadda Ake Wasa

Yara za su toni rami mai ɗan matsakaicin zurfi (ƙarami). Sai kuma kowa ya ja layi daga jikin wannan rami zuwa saitin gabansa. Layin zai kasance an ɗanyi masa gurbi ne. Wato an tona ya ɗan shiga cikin ƙasa kaɗan. Sannan tsawon layin gaban kowa zai kasance daidai da na‘yanuwansa.

Daga nan kowa zai samo ‘yarsa, wato ɗaya daga cikin abubuwan da aka bayyana ƙarƙashin ‘i’ na 5.35.2. Wani lokaci kuma akan yi amfani da ‘ya guda ɗaya ne. Wanda zagayensa ne a wasa zai aje wannan ‘ya a ƙarshen layi ta gabansa. Sannan zai ɗilla ta da yatsa da niyar ta shiga cikin ramin da aka tona a tsakiya. Idan ya samu nasarar saka ta ciki, zai yi zane a gabansa da tsinke. Yawanci akan ƙayyade tsawon tsanen da mutum zai yi yayin da ya ɗilla‘ ya cikin rami. Zanen kuma yakan kasance jan layi ne.

Yayin da mutum ya faɗi kuma, zai ba wa na gabansa ya don shi ma yayi. Haka yara za su yi ta jan layuka yayin da suka ɗilla ‘ya, har sai sun zana allo a gabansu. Wani lokaci kuma akan zana babban gidan dara na, sannan a masa layuka biyu, daga kusurwa zuwa kusurwa.

5.35.4 Tsokaci

Wannan wasa yana samar da nishaɗi ga yara. Hanya ce da ke sanya musu ƙwarewa wurin saiti da kuma nitsuwa. Domin dole sai da nitsuwa kafin yaro ya iya dilla ‘ya cikin ramin da aka tuna.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments