Ticker

6/recent/ticker-posts

Fanka

5.33 Fanka

Wannan wasa ne na yara maza. Masu gudanar da wasan fanka dole su kasance a bibbiyu. Yawan masu wasa na farawa daga huɗu zuwa sama. Wato zai kasance huɗu ko shida ko takwas da makamancin haka. Wasan na dandali ne. Saboda haka an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

5.33.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Daga nan za su rirriƙe hannuwan juna. Sai kuma kowa ya lanƙwashe ta baya tamkar wanda zai kwanta (ta baya). Sai kuma su yunƙura su riƙa juyawa a yadda suke haka, tamkar dai farfelar fanka. Haka za su yi ta juyawa har lokacin da mutum ɗaya ya gaji ko ya suɓuce ya faɗi. Daga nan fanka za ta wargaje.

5.33.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana buƙatar jarumta da rashin tsoro. Bayan haka, wasan na samar da nishaɗi tsakanin yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments