5.32 Wur-Wur
Wannan wasa ne na yara maza. Yara biyu ma kacal na iya gudanar da wannan wasa a tsakaninsu. Sai dai wasu lokutan akan samu yawan yaran ya fi haka. Wasa ne na tsaye, wadda kuma ba ta da waƙa. Sai dai ana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.
5.32.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Babu wani takamaiman wuri da ya keɓanta ga wasan wur-wur. Akan gudanar da wannan wasa a gida ko a dandali ko a duk wani wuri da masu wasa suka haɗu.
ii. Babu wani takamaiman lokacin da ya keɓanta na gudanar da wasan wur-wur. Akan yi shi da safe ko da hantsi ko da rana ko da yamma ko ma da dare idan akwai haske kusa.
5.32.2 Kayan Aiki
i. Ƙwanƙwalati
ii. Zaren buhu
5.32.3 Yadda Ake Wasa
Yara sukan nemi ƙwanƙwalati, sai su dandaƙe da dutse yadda zai buɗe ya yi faɗi kamar faifayi. Daga nan za a yi masa ɓuli guda biyu a tsakiya. Sai kuma a samo zaren buhu a cusa ta ɓuli ɗaya. Idan ya fito sai a lanƙwasa shi a mayar da shi ta ɗaya ɓulin, a kuma ɗaure ƙarshen. Idan aka yi haka, to an samar da abin da ake kira wur-wur.
Daga nan mai wasa zai riƙa sanya yatsunsa a cikin zaren daga gefe da gefen wurwur ɗin. Sai kuma ya jujjuya shi yadda zai nannaɗe saboda idan ya ja ya tashi; wato ya fara wainuwa da sauri sannan da ƙarfi. Farin cikin yaro da burinsa shi ne wur-wur ɗinsa ya yi zan-zan.
Da wannan wurwur ne yara suke karawa. Yaron da ke neman abokin karawa zai furta:
“Da wa za mu kara?”
Yadda ake karawar kuwa shi ne: Yara za su fuskanci juna. Sai kuma kowa ya matso da wur-wur ɗinsa da nufin tsinka zaren abokin karawarsa. Hakan na faruwa yayin da faifan ƙwanƙwalatin wur-wur ɗin ya taɓa zaren abokin karawa. Shi ya sa yara suke ƙoƙarin kaifa ƙwanƙwalatin saboda ya kasance mai kaifi.
5.32.4 Tsokaci
Wannan wasa ya kasance tamkar gasa a tsakanin yara. Burin kowane yaro shi ne ya tsinka wur-wur ɗin abokin karawarsa. Wasan yana samar da nishaɗi tsakanin yara.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.