Ticker

6/recent/ticker-posts

Kofi

5.34 Kofi

Wannan wasa  ne na yara maza. Adadin masu gudanar da wannan wasa na farawa daga biyu zuwa sama da haka. Wasa ne na zaune wanda ba ya da waƙa a cikinsa. Sannan ba buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.34.1 Wuri Da LokacinWasa

i. Babu wani ƙayyadadden wuri da aka fi gudanar da wannan wasa. Akan yi wasan a dandali ko ƙofar gida ko ma cikin gida, ko kuma wani wuri da yara kan taru.

ii. Wannan wasa ne na damina, lokacin da ƙasa take da damshi. Akan gudanar da wasan da hantsi ko da yamma. Ba a yin sa da dare.

5.34.2 Yadda Ake Wasa

Akan yi amfani da ƙaramin itace ko dutse ko wani abu makamancin wannan domin a riƙa kartar ƙasa har sai an yi wani dogon layi mai lauye-lauye wato tafiyar maciji. Daga nan za a sa ya tsaya su mulmule cikin ramin tamkar daɓe, yadda babu ƙasa da zai tsaya cikinsa. Daga nan mai tafiya zai zauna a gaban farkon layin, sannan ya ɗora yatsarsa guda a farkon layin. Abokin wasansa kuma zai zauna bayansa sannan ya rufe masa idanuwa. Daga nan wanda aka rufe wa idanuwan zai fara tura yatsarsa gaba yana bin daidai layin da aka shata. Zai riƙa cewa:

“Kofi.”

Wanda ya rufe masa ido kuwa zai riƙa cewa:

“Yes.”

Haka zai ci gaba da bin layin sannu a hankali cikin taka tsantsan domin kada ya fice da yatsarsa daga cikin layin. Da zarar ya wuce kuwa, to ya faɗi. Saboda haka zai tashi, wanda ya rufe masa ido kuma zai zo ya zauna shi ma ya gwada tasa bajinta.

5.34.3 Tsokaci

Wannan wasa yana buƙatar natsuwa. Idan babu natsuwa, mai yin kofi ba zai je ko ina ba zai faɗi.Sannan wasan na samar da nishaɗi ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments