5.31 ‘Yar Cille
Wannan wasa ne da aka fi gudanarwa a lokacin damina. Yara biyu ma kacal za su iya wannan wasa a tsakaninsu. Amma yawansu na iya ɗara haka. Wasan na tsare ne wanda ba shi da waƙa. Amma akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi.
5.31.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Akan nemi wuri mai yalwar faɗi domin gudanar da wannan wasa. Yawanci wurin na kasancewa inda jama’a ba sa yawan wucewa.
ii. Akan yi wannan wasa da hantsi ko da yamma.
5.31.2 Kayan Aiki
Gajeren kara ko sisirin bushasshen itace a matsayin ‘yar cilli.
Siririn bushasshen itace mai madaidaicin tsawo a matsayin icen bugu.
5.31.3 Yadda Ake Wasa
Da farko dai za a zana babbar da’ira a ƙasa, ta hanyar amfani da kara ko wani itace. Daga nan kuma za a je tsakiyar wannan da’irar a toni wani ƙaramin rami marar zurfi wanda tsawonsa bai fi ɗaya bisa ukun kamu ɗaya ba. A gaban wannan da’ira kuwa, za a zana wani layi wanda ke iyakance mai kamawa da kuma mai cilli. Akan kira wannan layi da suna iyaka. Daga nan wanda zai fara wasa zai shiga cikin wannan da’ira. Zai sanya ‘yar cilli bisa wannan rami a ranga-ranga. Abokin wasansa kuwa zai je can gaban da’ira ya tsaya, ya riƙa fuskantar wanda zai yi cilli. Mai yin cillin zai sanya icen bugun da ke hannunsa a cikin ƙaramin ramin, daidai ƙasar ‘yar cilli.
Daga nan zai cilla ‘yar cilli iyaka ƙarfinsa. Mai kamu kuma da ke can tsaye, zai yi ƙoƙarin kama wannan ‘yar cilli da aka cillo. Idan har ya kama ta, to mai cilli ya faɗi. Idan kuwa bai kama ba, to zai jefo ‘yar cillin da niyyar ta sauka cikin da’irar da aka zana. Shi kuwa mai cilli zai yi ƙoƙarin buge ta da sandar bugun da ke hannunsa. Idan har ta faɗa cikin wannan da’ira, to mai bugu ya faɗi, don haka mai kamu zai karɓi wasa. Idan kuwa ya buge ta har ta fita daga cikin da’irar, to zai je ya ƙirgo daga wurin da ‘yar cillin ta faɗi zuwa daidai kan ramin cilli.
Yadda ake ƙirge kuwa shi ne, za a yi amfani da sandar bugu a riƙa kwantar da ita a ƙasa tamkar dai ma’aunin rula. Za a ci gaba da ƙirga tsawon sanda-sanda da ke tsakanin wurin da ‘yar ta faɗi har zuwa jikin ramin cilli. Yayin da aka kamala wannan ƙirge sai kuma a ci gaba da cilli.
A lokacin da mai kamu ya cillo, mai bugu kuma ya buge ‘yar cilli, sai aka yi rashin sa’a mai kamu ya kama ‘yar kafin ta taɓa ƙasa, to duk lissafin da mai bugu ya yi a baya ya zube. Sannan ya faɗi. Saboda haka zai fara lissafi ne daga ɗaya yayin da yin sa ya zagayo.
5.31.4 Wasu Dokokin Wasa
i. Idan mai cilli ya yi cillin da ba ta bar cikin da’ira ba, to ya faɗi.
ii. Idan mai kamu ya kama ‘yar cilli yayin da aka cilla ta, to mai cilli ya faɗi.
iii. Idan mai kamu ya wurgo‘ya ta faɗa cikin da’ira, to mai cilli ya faɗi.
iv. Idan mai kamu ya kama ‘yar cilli yayin da mai bugu ya buge ta kafin ta je ƙasa, to mai cilli ya faɗi kuma makinsa gaba ɗaya ya zube.
v. Yayin da ‘yar cilli ta hau kan layi a lokacin cilli ko jefowa, to za a sake.
5.31.5 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana buƙatar ƙwarewa da bajinta. Yana kuma samar da nishaɗi ga masu wasan.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.