5.30 Dokin Kara
Wannan wasa ne na yara maza. Yara kimanin goma zuwa sama da haka ne suke taruwa domin gudanar da wannan wasa. Wasan ya kasance kwaikwayo ga hawan daba da sauran hawa makamantan wannan, da yara ke ganin manya suna gudanarwa. Ba ya tafiya da waƙa, amma akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi.
5.30.1 Wuri Da Lokacin Wasa
i. Wannan wasa ba wuri guda ake gudanar da shi ba. Yawanci masu wasa sukan zaga unguwanni ne.
ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma.
5.30.2 Kayan Aiki
i. Karan dawa mai ƙarfi
ii. Ƙyallaye
iii. Ƙusa
iv. Igiya
5.30.3 Yadda Ake Wasa
Masu wasa sukan nemi kararen dawa masu ƙarfi. Daga nan za su yanki gaɓoɓi daga jikin wani karan na daban, su yi amfani da ƙusa su laƙa a jikin dogon kara mai ƙarfi da suka samu a matsayin doki. Sai kuma su samo ƙyallaye su yi wa dokin kwalliya. Akan yi amfani da igiya a matsayin linzami.
Bayan nan yara sukan naɗa matsayi a tsakaninsu. Akan zaɓi sarki da galadima da waziri da wasu matsayin masu kama da wannan. Daga nan yara za su ɗunguma a kan waɗannan dawakai su riƙa zagaya unguwanni. Wani lokaci sukan yi sukuwa, wani lokaci kuwa su tafi a hankali. Waɗanda suka yarda da ƙarfin karan dawar da suke amfani da shi, sukan yi taɓarya. Wato su kafa karan a tsaye sannan su ɗangalafe. Wasu kuwa dawakin suna karyewa a yayin da suka yi taɓarya.
Haka yara za su ci gaba da yi har lokacin da suka gaji. Wani abin burgewa shi ne, masu wasan sukan bi umarnin sarki tamkar dai a hawan dawakin gaske.
5.30.4 Tsokaci
Wannan wasa ne na motsa jiki ga yara. Sannan ya kasance tamkar hoton hango al’adar Bahaushe ta hawan dawaki. Yara sukan koyi halayya da ɗabi’un shugabanci da lamuran da suka shafi fada.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.