Ticker

6/recent/ticker-posts

Bigo

5.29 Ɓigo

Wannan ma wasa ne na yara maza da ke cikin rukunin wasannin dandali. Ba ya tafiya da waƙa, sannan kayan aikin da take buƙata kawai shi ne riguna. Yara na nannaɗa rigunansu domin amfani da su wurin duka. An fi gudanar da wasan da dare, musamman lokacin farin wata.

5.29.1 Yadda Ake Wasa

Yara sukan rabu gida biyu. Adadin yaran na kasancewa daidai da na juna. Sai dai idan guda ɗaya ya haura, wato ba shi da abokin da za a raba su da shi, akan samu gida guda ya fi guda yawan ‘yan wasa.

Bayan komai ya kammala, za a zana layi guda ɗaya a tsakiyar ɓangarorin biyu na masu wasa. Wato layin zai kasance yara ba tsakaninsu, yayin da suke fuskantar juna. Yaran ɓangaren da za su fara wasa za su cire rigunansu su nannaɗe, daɗin duka. Sai kuma su fara furucin farkon wasa, yayin da abokan wasansu na tsallaken layi ke amsawa. Ga yadda abin yake:

Masu Duka: Ɓigo

Abokan Wasa: Ɗaya

Masu Duka: Ɓigo

Abokan Wasa: Biyu

Masu Duka: Ɓigo

Abokan Wasa: Uku

Da zarar an kai ga ambata uku, masu duka za su yi ƙoƙarin hana abokan wasansu tsallako layi. Su kuwa abokan wasan, burinsu shi ne su tsallako layi su dawo ɓangaren masu duka. Masu duka za su riƙa bugu da rigunan da suka nannaɗa. Yayin da suka kama ɗaya daga cikin abokan wasan nasu, to ya zama ɗan gidansu. Ke nan yawan abokan wasan nasu ya ragu. Idan kuwa ɗaya daga cikin abokan wasan nasu ya samu dammar tsallako layin da aka zana, to ya tsira.

Wani lokaci yara na runtuma da gudu zuwa wuri mai nisa. Har ma sukan zagayo ta lungunan gidaje masu ɗan nisa a wasu lokuta. Yayin da aka kama na kamawa, waɗanda suka tsallako kuma suka tsallako, to za a sake wasa daga farko. Amma wannan karon, ɓangaren da suka yi duka ba su za su koma ba.

5.29.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar musu da nishaɗi. Baya ga haka, yana koya musu jarumta da juriya da kuma dabara. Wasu yaran na jure bugun da ake musu sannan su kurɗa da ƙarfin tsiya har sai sun tsallaka layin zuwa ɓangaren masu bugu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments