Ticker

6/recent/ticker-posts

Yaki

5.23 Yaƙi

Wannan wasa ne na yara maza. Yara masu yawa ne suke taruwa domin gudanar da wannan wasa. Domin kuwa akan yi wasan ne tsakanin unguwanni biyu ko ma sama da haka. Wasan ba ya tafiya da waƙa, sai dai akan bukaci kayan aiki yayin gudanar da shi. Yakan kasance a wani keɓaɓɓen fili, ko lungun da mutane ba su fiye bi ba.

5.23.1 Kayan Aiki

Yayin gudanar da wannan wasa akan yi amfani da kayan aiki iri-iri. Wannan ya danganta da irin abubuwan da yaran ke da damar mallaka a lokacin wasan. Daga cikin kayayyakin da ake amfani da su yayin wasan yaƙi akwai:

i. Barkwanon tsohuwa

ii. Ya’yan tsiron zaƙami

iii. Riguna da sauransu 

5.23.2 Yadda Ake Wasa

Wasan yakan kasance ne tsakanin ɓangarori guda biyu. Yawanci ‘yan wasan kowane ɓangare na fitowa ne daga unguwa guda. Akan yi amfani da kayan yaƙi da aka lissafo a sama yayin fafatawa. Kowane ɓangare muradinsu shi ne su fi ƙarfin abokan karawarsu.

Akan yi amfani da ‘ya’yan zaƙami wajen jifa daga nesa. A irin waɗannan lokuta, waɗanda suke da ‘ya’yan zaƙamin da yawa kuma suka iya jifa sosai, sukan ci nasara ta hanyar korar abokan karawa fata-fata. Wannan na faruwa musamman lokacin da ‘ya’yan zaƙamin abokan karawar tasu suka ƙare. Sai dai masu wasa kan tsini ‘ya’yan zaƙamin da abokan karawa suka jefe su da su. Amma a yayin tsinar, za a iya cim musu.

Barkwanon tsohuwa kuwa akan yi jifa da shi ko a baɗa wa abokan karawa yayin da ake kusa da kusa. Waɗanda aka baɗa wa barkwanon tsohuwa za su kasance suna tari da hacitawa, ga kuma zafi da zogi da idanunsu zai riƙa yi.

Riguna kuwa akan naɗe su ne daɗin duka. Yayin da ake kusa da kusa da abokan karawa, za a riƙa dukan juna da riga. Wani abun ban sha’awa shi ne, duk irin doke-doken da za a yi, rai ba ya ɓaci. A maimakon haka, kowane ɗan wasa na sawa a ransa cewa, wasa ake yi. Yayin da abin ya so ɓaci tsakanin yara biyu, yaran da kansu za su haɗu domin raba faɗan. Daga ƙarshe, duk ɓangaren da suka yi nasara, za su kasance cikin farin ciki da tinƙaho. Yayin da aka haɗu filin wasa, za su riƙa gori a yaran da suka kora wurin yaƙi. Su kuwa yaran za su riƙa ba da Dalilan waskiya game da abin da ya sa suka nuna gazawa wurin yaƙin. Wani lokaci za su riƙa cewa: “Hir a sake yi.” Daga nan za a sake sanya ranar da za a yi wani yaƙin.

5.23.3 Tsokaci 

Haƙiƙa wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan babbar hanya ce ta koyar da yara jarumta da juriya da kuma dabarun kare kai, tare kuma da dabaru da hikimomin gallabar abokin karawa. Wasan dai kwaikwayo ne na yaƙi. Sannan yana samar da nishaɗi ga yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments