Ticker

6/recent/ticker-posts

Jirgi 2

5.22 Jirgi 2

Wannan wasa ne na yara maza ta tsaye, wadda kuma ba ta da waƙa. Yara uku ne ke gudanar da wannan wasa. Saboda haka, idan masu wasa suka kasance da yawa, kowa zai kama abokan yin jirginsa, wato dai su kasance uku-uku. Ba a buƙatar kayan aiki yayin gudanar da ita. Sannan wasa ce ta dandali wadda aka fi gudanarwa da dare, musamman lokacin farin wata.

5.22.1 Yadda Ake Wasa

Yaro guda mai ƙarfi zai tsaya. Wani guda kuma zai hau bisa kafaɗunsa ya zauna, ya miƙo ƙafafunsa ta gaba. Yaro na uku kuwa zai ɗaga ƙasa da hannuwansa, sannan ya ɗago ƙafafunsa zuwa daidai cikin yaro na farko da ke tsaye. Wannan shi ake kira farfela. Yaron da ke tsaye zai kasance tsakanin ƙafafun, sannan zai riƙe su da hannuwa biyu. Daga nan sai yaron da ke zaune bisa kafaɗun na tsaye ya sanya ƙafafunsa cikin hamatar wanda ya dafa hannuwa ƙasa, wato farfela. Farfela kuwa zai riƙe ƙafafuwan sosai yadda ba zai suɓuce ba.

Yayin da komai ya kammala, jirgi ya haɗu ke nan. Yaron da ke tsaye zai riƙa hajijiya da su gaba ɗaya. Wani lokaci sukan zube ƙasa yayin da aka samu wani kuskure. Yayin da aka samu gwanaye, farfela kan sake ƙafafun da ke maƙale a hamatarsa, ya ware hannuwan yayin da ake ta juyi da su.

5.22.2 Tsokaci

Wannan wasa na ɗaya daga cikin wasannin ƙiriniya na yara maza. Sai dai yana sanya musu jarumta da juriya da rashin tsoro. Sannan yana samar da nishaɗi gare su.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments