Ticker

6/recent/ticker-posts

Dandukunini/Dandukununu

5.21Ɗanduƙunini/Ɗanduƙununu

Wannan ma wasan yara maza ne da ke cikin rukunin wasannin tashe. Kayan aikin da ake buƙata domin gudanar da shi sun haɗa da igiya da kuma bula ko baƙin bayan tukunya. Kimanin yara biyar ne zuwa sama da haka ke gudanar da wasan. Sannan tana tafiya da waƙa. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashen ƙasar Hausa, an fi gudanar da wannan wasa da dare, bayan an sha ruwa.

5.21.1 Yadda Ake Wasa

Ɗaya ɗaya daga cikin yara zai tuɓe riga ya tsaya daga shi sai wando. Idan ma ƙarami sosai ne, wandon yakan kasance ɗan ƙarami sosai. Sai kuma a mulke masa jiki da bula ko baƙin bayan tukunya. Za kuma a ɗaura masa igiya a ƙugu. Wannan yaro shi ake kira Ɗanduƙunini. Ɗanduƙunini zai shige gaba sauran yara na biye. Yaro guda kuma zai riƙe ƙarshen igiyar da aka ɗaura wa Ɗanduƙunini.

Yayin da aka je wurin wasa, Ɗanduƙunini zai sanya waƙa. Sauran yara kuwa za su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take:

Ɗanduƙunini: Ɗanduƙunini,

Yara: Sai an ba ka.

 

Ɗanduƙunini: Ni da gidanmu?

Yara: Sai an ba ka.

Ɗanduƙunini: Gidan na ubana?

Yara: Sai an ba ka.

 

Ɗanduƙunini: Gidan na uwata?

Yara: Sai an ba ka.

 

Ɗanduƙunini: Ku bar ni na ɗiba,

Yara: Sai an ba ka.

 

Ɗanduƙunini: Kar ku hana ni,

Yara: Sai an ba ka.

 

Ɗanduƙunini: Ni da gidanmu?

Yara: Sai an ba ka.

Yayin da ake wannan waƙar, Ɗanduƙunini zai riƙa zabura domin ɗaukar wani abu da ke gabansa. Amma sai wanda ke riƙe da igiyar da aka ɗaura masa ya jawo shi baya. Haka dai za a ci gaba, Ɗanduƙunini yana ta ƙoƙarin ɗaukar wani abu, amma ana hana shi.

5.21.2 Tsokaci

Wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan yana ɗauke da darasi da ke nuna cewa, kasancewar, ba daidai ba ne mutum ya ɗauki abu ba tare da an ba shi ba, ko da kuwa yana da gadara da wannan abu. Wato kamar dai yadda duk da Ɗanduƙunini a gidansu ya yi niyyar ɗaukar wani abu, an hana shi, an ce ya bari sai an ba shi.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments