Ticker

6/recent/ticker-posts

Dokin Almajirai

5.19 Dokin Almajirai

Wannan wasa ne na nishaɗi da kuma motsa jiki da yara maza ke gudanarwa a dandali. Yara uku ne zuwa sama da haka ke gudanar da wannan wasa. Ana gudanar da wannan wasa ne a dandali, saboda haka da dare aka fi gudanar da shi, musamman lokacin farin wata.

 

5.19.1 Yadda Ake Wasa

Yaro guda zai tsaya. Sai wani kuma ya ɗaga kafaɗunsa daga baya sannan ya sunkuya. Sannan wani yaron daban zai hau bayan wanda ya sunkuya ɗin. A haka wanda ke tsaye da kuma wanda yake sunkuye za su riƙa tafiya, yayin da wanda ya sa wa zai riƙa ba da waƙa su kuma suna amsawa kamar haka:

Bayarwa: Dokin almajirai,

Amshi: Sukuta.

 

Bayarwa: In ba sukutan ba,

Amshi: Sukuta.

 

Bayarwa: Yau na hau jaki,

Amshi: Sukuta.

 

Haka za su je iyakar wurin da aka ƙayyade za a riƙa zuwa a wasan sannan su dawo. Daga nan kuma na saman sai ya sauka wani ma ya hau. Haka za a ci gaba da yi har sai an yi wa kowa.

 

5.19.2 Tsokaci

Wannan wasa hanya ce ta motsa jiki ga yara. Sannan yana samar da nishaɗi gare su.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments