Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Reni

5.18 Allah Reni

Wannan ma wasa ne na dandali. Misalin yara biyar zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Yawan mutanen zai iya kaiwa goma ko ma sama da haka. Yana tafiya da waƙa, sannan akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Kasancewar wasan na dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata. Kayan aikin da ake nema yayin gudanar da wasan su ne kallabi ko tsumma.

 

5.18.1 Yadda Ake Wasa

Mutum ɗaya zai zauna ya miƙe ƙafafunsa. Wannan shi ake kira Allah raini. Wani yaronmu ma zai tsaya a bayansa ya rufe masa idanu. Idan ana amfani da kallabi ko tsumma, to da shi za a rufe idanu. Idan kuma babu, to akan rufe ne da hannuwa. Sauran yara kuwa za su jeru a layi. Daga nan wanda ya rufe wa Allah raini ido zai yi inkiya da baki cewa a taho a tsallaka ƙafafunsa. Yaron da ke tsaye a layi zai taho a hankali ya tsallaka shi. Daga nan kuma sai wanda ya rufe wa Allah raini ido ya tambaye shi:

“Allah raini wa ya tsallaka ka?”

 

Shi kuma zai ambaci sunan wanda yake tunanin shi ne ya tsallaka shi. Idan ya faɗa daidai, to zai tashi. Wanda aka ambaci sunan nasa kuwa zai zo ya zauna, wato ya zama Allah raini. Idan kuwa bai faɗi sunan daidai ba, to wani daban zai zo ya tsallaka. Wani lokaci wanda ya rufe wa Allah raini ido zai iya ishara da baki cewa kada kowa ya tsallaka. Sannan sai ya tambaya Allah raini wanda ya tsallaka shi. A nan idan ya ce: “babu,” to ya yi nasara. Idan kuwa ya ambaci sunan wani daban, to ya faɗi.

 

Idan yara suka gama tsallaka shi baki ɗaya ba tare da ya gane wanda ya tsallaka shi ba, to wanda ya rufe masa ido zai ba da dama ga yara su je su ɓuya. Yayin da yara suka ɓuya, wanda ya rufe masa ido zai ambaci wuraren da suka ɓuɓɓuya. Amma ba zai fayyace takamaimai da sunan waɗanda suka ɓuya a wuraren ba. Misali, wanda ya rufe wa Allah Raini ido zai ce:

“Bayan bishiya, bayan dakali, gefen alamanke …”

Sai kuma a tambayi Allah raini ya faɗi sunayen waɗanda suka ɓuya a waɗannan wurare. Shi kuwa zai yi ƙoƙarin yin hakan. Misali zai ce:

“Musa ne a bayan bishiya.”

Idan ya faɗa daidai to za a ce wa Musa:

“Taho bisa sayyadarwa.”

Idan kuwa bai faɗa daidai ba, to za a ce Allah raini ya je ya goyo shi ya tafo da shi.

 

5.18.2 Wasu Dokokin Wasa

i. Duk wadda Allah raini ya ambaci sunansa bayan ya tsallaka shi (ya tsallaka Allah raini), to shi ne zai zama Allah raini.

ii. Yayin da Allah raini ya fahimci ba a tsallaka shi ba, kuma ya faɗi hakan, to wanda ya ƙi tsallakawar shi ne zai zama Allah raini.

iii. Idan mutane suka gama tsallake Allah raini ba tare da ya ambaci sunan kowa ba, to za su je su ɓuya.

iv. Yayin da Allah raini ya ambaci sunan wani ɗan wasa a matsayin ya ɓuya a wani wuri, sai kuma aka yi rashin dace ba a nan ya ɓuya ba, to zai je ya goyo wanda ke ɓoye a wannan wuri.

v. Wanda aka ambaci sunansa da wurin da ya ɓuya, to shi ne zai zama Allah raini.

 

5.18.3 Tsokaci

Wannan wasa yana koyar da nazari da zurfafa tunani tare da nutsuwa ga yara. Dole ne Allah raini ya kasance ya yi amfani da basira da zurfafa tunani kafin ya iya tantance wane ne ya tsallaka shi, ko kuma ya gane ba a tsallaka shi ba.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments