Ticker

6/recent/ticker-posts

Damo Riya Damo

5.17 Damo Riya Damo

Wannan ma wasa ne da ke da zubi da tsarin jini da jini da kuma noti-noti. Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ke cikin kowace wasa. Waƙar damo riya damo ta kasance kamar haka:

Bayarwa: Damo riya damo,

Amshi: Damo!

 

Bayarwa: Damo ɗan hajiya,

Amshi: Damo!

 

Bayarwa: Mu je Katsina da kai,

Amshi: Damo!

 

Bayarwa: Mu lafto kanwa,

Amshi: Damo!

 

Bayarwa: Mu kai wa hajiya,

Amshi: Damo!

Bayarwa: Ta ɗanɗana ta ji,

Amshi: Damo!

 

Bayarwa: Sauran wani ya faɗa.

Yayin da aka kawo wannan gaɓa, duk wanda ya ambaci damo to ya ɓata, saboda haka hukuncin wasa ya hau kansa tamkar yadda aka tattauna a sama, cikin bayanin wasan jini da jini.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments