Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.6.1.1 Ɗan Amina.
Jagora: Ya
bisimilla Allah.
Amshi: Ɗan Amina.
Jagora: Za ni yabon
Muhamman.
Amshi: Ɗan Amina.
Jagora: Mai birnin
Madina Mamman.
Amshi: Ɗan Amina.
Jagora: Ina masoya
Muhamman.
Amshi: Ɗan Amina.
Jagora: A ba mu
domin Allah.
Amshi: Ɗan Amina.
(Ɗan Amina)
Wannan waƙar a cikin taro mabarata suke aiwatar da ita sadda suke bara, amma kuma sau
da yawa akan sami mai bara shi kaɗai yana rera ta. Haka kuma, a mafi yawan lokuta mabarata mata ne suka fi
amfani da ita. Idan aka lura waƙar ta begen
Annabi Muhammadu ce (SAW). Ga ƙarin misalin
wata waƙar mai suna “Mu Tai Bara”.
0 Comments
Post your comment or ask a question.