Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
(Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
4.6.1.2 Mu Tai Bara
Jagora:
Mu tai bara don Allah,
Amshi: Saboda
Manzon Allah.
Jagora: Ku taimaka
don Allah,
Amshi: Saboda
Manzon Allah.
Jagora: Allah sa
muje gida dan Allah,
Amshi: Saboda
Manzon Allah.
Jagora: Allah kare
tsautsayi da hasara,
Amshi: Saboda
Manzon Allah.
Jagora: A bamu
domin Allah,
Amshi: Saboda
Manzon Allah.
Ita kuwa wannan waƙar in
an lura bara ne tsagwaronsa ba tare da surka waƙar da wani bege ba. Ita ma a cikin taro mabarata ke amfani da ita. A mafi
yawan lokuta ƙungiyar
mabarata da ke amfani da wannan waƙar takan haɗa masu naƙasa dabam-daban, kamar kutare da makafi da guragu da ma wasu gajiyayyu waɗanda ba su da wata naƙasa. Ita ma wannan waƙar wani daga cikin mabaratan ke bayarwa saura na amsa masa. Ga kuma wata
mai suna Maula ta Sidi:
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.