Ticker

6/recent/ticker-posts

3.6 Kammalawa - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 110)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.6 Kammalawa

Kamar yadda aka ambata a sama, wannan rukuni ya rattabo misalan waƙoƙin gargajiya na Hausawa ne, ba tare da feɗe su ba. Saboda haka, akwai buƙatar nazartar kowace daga cikin waƙoƙin domin fitar da jigo da salailai da kuma falsafofi da za a iya tararwa ciki. Da ma dai, waƙoƙin gargajiya na Hausa sun kasance tamkar makaranta da ke koyar da darussa iri-iri da suka shafi faɗakarwa da nishaɗantarwa da ilimantarwa da koyar da dabarun zaman duniya da makamantansu. Za a ci karo da waɗannan jigogi yayin da aka nazarci waƙoƙin ɗaya bayan ɗaya.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments