Ticker

6/recent/ticker-posts

3.4 Kitso - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 104)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.4 Kitso 

Kitso hanya ce ta tsaftace gashi da gyara shi. Bayan an taje gashi, akan ƙuƙƙulla shi cikin salo ko tsari mai kyau. Akan ɗauki tsawon lokaci kafin a kai ga kammala wa mace guda kitso; wanda hakan ya danganta da salon kitson da ake yi. A maimakon zaman shiru, akwai waƙoƙi da akan rera yayin kitso domin ɗebe kewa da samar da nishaɗi. Wannan zai sa a kammala kitso ba tare da ƙosawa ba. Daga cikin waƙoƙin kitso akwai:

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments