Ticker

6/recent/ticker-posts

3.3 Kaɗi - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 102)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.3 Kaɗi

Kaɗi hanya ce ta yin amfani da mazari wajen sarrafa auduga domin samar da zaren da ake amfani da shi wurin yin tufafi ko gyara tufafin da aka riga aka yi. Manyan mata aka fi sani da sana’ar kaɗi. A lokacin kaɗi, mata kan yi waƙoƙi daban-daban. Misalai daga ciki sun haɗa da:

3.3.1 Allah Ba Ni Kaɗa

Kamar dai yadda aka bayyana a babi na farko, wannan waƙa na ɗauke da addu’ar alkairi. Mai waƙar na fatan samun kaɗa domin ta yi zaren kanta, saboda ta ɗinka wa masoyinta kaya. Ga yadda waƙar take. 

Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: In yi zare na kaina,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: In yanke zugage,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: Dela nan tara nan talatin,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: Allah ba ni kaɗa,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

 

Bayarwa: In wa masoyi riga,

Amshi: Dela ba Dela ba Kande.

 

Bayarwa: In wa masoyi wando,

Amshi: Ayeye ye ranaye.

3.3.2 Amadu

Wannan ma waƙa ce da ta shafi kaɗi. Mai waƙar na yabon wani mai suna Amadu. Za a iya samun canji ga wannan suna, wanda hakan ya danganta da wuri da kuma mai rera waƙar. Wasu na iya amfani da sunan masoyansu a cikin waƙar. Ga yadda ake rerata:

Ayye yaraye zare nake yi,

Ayye yaraye nanaye.

 

Amadu kundu Amadu siliya,

Amadu kundu aska tara.

 

A kowas ya faɗa mini Amadu,

Na ce riga ni ka yo masa.

 

Mai aska tara, wando ni kai masa,

Hulla ni kai mai, mai aska tara.

 

Bana rawani ni kai masa,

Aljanna kusa faɗawa mu kai.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments