Ticker

6/recent/ticker-posts

2.2 Wasannin Yara Mata Na Dandali - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 71)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.2 Wasannin Yara Mata Na Dandali 

Waɗannan wasanni ne da yara mata ke gudanarwa a dandali. An fi gudanar da waɗannan wasanni da dare, musamman lokacin farin wata. Su ake kira da wasannin gaɗa. Mafi yawan wasannin gaɗa suna tafiya da waƙoƙi. Waƙoƙin kan ƙunshi bayyana muradin zuci (na masu wasa) da hannunka-mai-sanda ga iyaye da sauran jama’ar gari da makamantan wannan. Za a kawo bayanan biyu daga cikin waɗannan wasanni da ke tafiya da waƙa, sannan a biyo bayansu da waƙoƙin wasannin dandali na yara mata ba tare da bayanin wasannin da ke ɗauke da waɗannan waƙoƙi ba.

2.2.1 Gamuna

Wannan wasan dandali ne na mata. Ana buƙatar yara da dama domin gudanar da wannan wasa. Saboda haka, yawan masu gudanar da wasan na kasancewa ashirin zuwa sama a mafi yawan lokuta.

2.2.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Akan gudanar da wannan wasa a dandali ko gidan biki ko wani wuri da ake samun taron yara mata.

ii. Akan gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma ko kuma da dare, lokacin hasken farin wata.

2.2.1.2 Yadda Ake Wasa

Masu wasa za su rabu zuwa gari biyu. Za a yi ƙoƙarin daidaita yawan ‘yan garuruwan guda biyu. ‘Yan gari ɗaya daga cikin garuruwan biyu za su tsuguna su dafa kafaɗun juna. ‘Yan ɗaya garin kuma za su koma can gefe, su ba su tazara. Daga nan za su tattauna tsakaninsu kan wadda za su ɗauka daga garin waɗanda suka tsuguna. Da zarar sun ƙare tattaunawa sai su dawo. Za su zo daf da waɗanda suke tsugune, yayin da suke dafe da kafaɗun juna. Yayin da suka zo, za su fara waƙa wanda a wannan lokaci ne kuma garin da ke tsugune za su tashi su riƙa ba su amsa. Haka za su riƙa yi suna rangaji tare da ‘yan taku zuwa gaba da baya. Waƙar ita ce kamar haka:

Masu Ɗauka: Ga mu nan muna zuwa,

 Muna zuwa muna zuwa,

 A cikin JSS Misau.

Masu Bayarwa: Meye dalilin zuwanku?

 Zuwanku zuwanku,

 A cikin JSS Misau?

 

Masu Ɗauka: Za mu ɗauki ɗayarku,

 Ɗayarku ɗayarku,

 A cikin JSS Misau.

Masu Bayarwa: Da sai ku faɗa mana sunanta,

 Sunanta sunanta,

 A cikin JSS Misau.

 

Masu Ɗauka: Da za mu ɗauki A’isha,

 A’isha A’isha,

 A cikin JSS Misau.

A wannan gaɓa za su kama wadda suka ambaci sunanta sannan su dawo da ita cikinsu. Daga nan kuma za su fara tsalle tare da faɗin:

Mu gidanmu ba yunwa,

Sai biredi sai shayi,

Sai abincin Turwa,

Abin da muke ci ba kwa ci.

Daga nan za su koma can nesa kaɗan su tsuguna. Garin da aka ɗauke musu ‘yar wasa kuma za su tattauna game da wadda za su ɗauko. Haka za a ci gaba da wasa har sai an gaji.

2.2.1.3 Tsokaci

Wannan wasa ne na nishaɗi tsakanin yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Waƙar wasan na nuna hoton ziyara tare da neman buƙatar ɗaukar ɗiya daga wani gida. A kaikaice, falsafar wannan waƙa na nuni ga neman aure da bayarwa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments