Ticker

6/recent/ticker-posts

2.1 Yara Maza - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 67)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.1 Yara Maza 

Waɗannan su ne wasannin da yara maza ke gudanarwa a dandali. An fi gudanar da irin waɗannan wasanni da dare musamman lokacin farin wata. Za a kawo misalan wasanni biyu da ke ɗauke da waƙoƙin gargajiya, sannan za a kawo sauran misalan waƙoƙi ba tare da bayanan wasannin da ke ɗauke da waƙoƙin ba.

2.1.1 Jini Da Jini

Wannan wasa ne na gargajiya. Misalin yara takwas ne zuwa sama suke gudanar da wannan wasa. Yana da sigar shugabanci na Liman da Ladan da kuma Mamu.

2.1.1.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Jini da jini wasan maza ne na dandali.

ii. An fi gudanar da wannan wasa ne da dare, musamman bayan an ci abincin dare.

2.1.1.2 Kayan Wasa

i. Rigar da aka nannaɗe wadda ake amfani da ita wajen dukan wanda ya ɓata.

ii. Bishiya ko katanga ko wani wuri da za a nuna a matsayin sha.

2.1.1.3 Yadda Ake Wasa

Liman yakan tsaya a gaba. Ladan kuma tare da Mamu za su yi sahu-sahu a bayan Liman. Dukkanin ‘yan wasa za su nannaɗe rigarsu, wadda da ita ce suke dukan duk wanda ya ɓata. Daga nan liman zai bayar da sanarwa kamar haka:

“Za a fara, za a fara!”

Ladan zai maimaita wannan sanarwa. Daga nan kuma Liman zai fara ambaton sunayen abubuwa ɗaya bayan ɗaya. Da zarar ya ambaci sunan abu, Mamu za su amsa da danja idan har abin yana da jini a jikinsa. Idan kuwa ba shi da jini, to za su amsa da babu. Yayin da wani yaron ya kuskure, to ya faɗi. Don haka za a rufa shi da duka da rigunan da aka nannaɗe a hannunsa. Ba za a bar shi ba har sai ya sha. Ladan ne yake da hurumin bayyana wanda ake duka ya sha ko bai sha ba. Da zarar Ladan ya bayyana cewa an sha, to za a dena duka. Daga nan kuma wanda aka daka shi ne zai kasance Liman a yayin ci gaba da wasa. Misali:

Liman: Jini da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Rago da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Akuya da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Kaza da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Zakara da jini,

Mamu: Danja!

 

Liman: Mota da jini.

Mamu: Babu!

Kamar yadda aka yi bayani a babi na farko, wannan waƙa na koyar da Natsuwa da mayar da hankali. Wato kamar dai yadda dole ne ɗan wasa ya natsu gudun kuskure wa dokokin wasa.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments