Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa. Ahmadu Bello University Press Limited.
Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:
Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369
1.3 Samuwar Bara
Bara ya fara samuwa ne a cikin
al’umma tun kafin a fara rubuta tarihi don ajiyewa (Jakson 2008: Google
search). Ana samun bara a mafi yawan al’ummomin duniya, amma hanyoyin da ake
gudanar da shi da yadda tsarinsa yake su ne suka bambanta. Kasancewar bara ba
sasbon abu ba kamar yadda Jakson ya nuna shi ya sa a wannan aiki ya dubi a wasu
nahiyoyi na duniya wato a wasu ƙasashe sannan
daga baya aka dubi yadda yake a wannan ƙasa
tamu da kuma a yankin nazarina, wato yankin ƙasar Hausa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.