Ticker

6/recent/ticker-posts

Yahuza Dan Sadisu Madobi

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Yahuza ɗan Sadisu madobi,

Kadarkon da ake kwatance,

 

Shimfiɗa

Mai halin da ake kwatance,

Mai darajar da ta zarci kifce,

Wanda ya kere sa'a da zarce,

Mai ilimin da ake ta zance,

Mai shuhurar da ake kwatance,

Wanda ake ta yabo a zance,

Rai ya daɗe na faɗi karamce,

Masu farar aniya a kwance,

Ba su ganin fitina a kwance,

Tsohon minister Yahuza na ce,

Za ka gama duniya a huce,

Ka ci tuwo da furarka huce,

Ba fitina da ake kwatance.

 

Ya masanin sirrin zukata, za ni yabo ga abin yabawa,

Duk zarafin da na tashi zan yi albada'u kai nakka sawa,

Mudabbiru mai juya yayi, ƙarfafi rarraunanka bawa,

Na bijiro da yabon masoyi Yahuza Sadisu ɗan Madobi.

 

Sha yabo masu abin yabawa cikamaki nasu annabawa,

Na yi riƙon igiya ta ƙauna Rabbu hana ni karo da ɓarna,

Da ahali na gida sahabbai da mabiyansa dare da rana,

Annabi ɗan Abdallah Ɗahe inda ka sa sawunka nab bi.

 

Za ni yabo a gurin masoyi Yahuza Sadisu ɗan Madobi,

Mai yakana da halin nagarta ba shi da tauyo koko aibi,

Mai daraja da halin yabawa ba nukusanu halinsa zan bi,

Mai haƙuri da hali na kyauta dukka abin da yake ana bi.

 

 

Khaliƙu kai na riƙa murabbi da tsugunon sujada a bauta,

Kai nika bi da biyan buƙata a rukuni na salo na bauta,

Dukka buƙatu na nufata kai nika kaiwa ka kau biya ta,

Ga ni da Sadisu ɗan Madobi yarda mu zam tamkar madubi.

 

Ga shigifa ta shiga a huta mai ɗamarar kishin talakka,

Ga inuwar tsuguna a huta mai darajar da ta zarce tamka,

Mai hikima shi ke da zance mai ɗamara shi ke da tufka,

Kai nasara Y. S. Madobi don talakawa kai suke bi.

 

A rububi wasu ke shige wasu ko a guguwar kaɗawa,

Wasu su rabu jikin mutane su bi su bayyana tasu baiwa,

Wani ko hali nai ka bi nai na haƙuri da son talakawa,

Don haka ba fa zuga nake ba babu kamar Y. S. Madobi.

 

A nazarin da ake kwatance da shi ake zaɓen zakara,

Da fari za a bi illiminka da nasabarka abar a lura,

Sai a bi yarda kake da hulɗa da sarafi na fito a fara,

Karkaɗa gaf!! Rukunin ga ukku babu guda da ya bar Madobi.

 

Yahuza Sadisu ga ilimmi ga shi da gogayya a aiki,

Shi muka ji murya ta ja mu kafin ya hau minista da aiki,

Sanda yake murya ta Jamus ya wuce tsararraki a aiki,

Ga shi mutum mai son mutane Yahuza Sadisu na Madobi.

 

Da isimullahil a'azzam Yahuza za ya hau kadarko,

Koko in ce shi ne kadarko masu bara ku taho da ƙoƙo,

Wanda ya je shi ya kwana a can ya dara masu shiri na sakko,

Sai kabara Y. S. Madobi inda ka sa sawunka an bi.

 

Kun ji rugum na aradu motsi mai rikitar da daba ta zabi.

Ga rugugi na aradu wannan in aka yi shi ya tashi zabi.

Mai ɗamarar fama Yahuza ja mu mu je tafiya muna bi.

Ga galabar bayi a yanzu da izinin Allahu Rabbi.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments