Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Keke Ta (Dr) Aliyu Namangi Zariya

Muna shukura ga Rabbal alamina

Da alherin da yai mana ba kaɗan ba.


Muna murna da mulkin Ingilishi

Zuwan da sukai ƙasarmu ba tai tsiya ba.


Zama zamaninsu ne aka zo da faifa

Kuɗi ba masu nauyaya aljihu ba.


Daɗa zarafinsu ne aka zo da jirgi

Ka je Makka ba da tashin hankali ba.


Sa'annan ga su Babur, ga su Mota

Da farko a da can ba mu san da su ba.


Izan tafiya ta faru ka nemi mota

Izan jirgi ba kui daidai da shi ba.


Izan kuwa babu Jirgi babu mota

Ka je da ƙafarsa ba keken tsiya ba.


Banni da Basukar ho, ɗan jidali

shaƙiyyi ba abin babba ya hau ba.


A Ɗanmahawayi nih hau sai ya bar ni

Tudun-Yakaji ban kawo gari ba.


Ya bar ni da jin jiki da zama a turba

Da ɗai ko juma'a ba a je da ni ba.


Kuɗi tirmis, na ba shi sule-da-sisi

keke bai mani rangwame ko da ɗari ba.


Na ce masa "Basukur riƙa sawwaƙewa"

Ya ce "Malam hala ba ka sanni ne ba".


Ina da tsiya biyar farkonsu fanca

Na kau buga bindiga ba mai wuta ba.


In babbake zuciya, in tafi da sawu

Cikin daji kamar ba a je da ni ba.


Muna tafiya kuma na fizge kaina

Mu faɗa kwazazzabo ni ban kula ba.


Ina da ciki ana ce mai kurumbo

Karambanin hawa ba ka saya ba.


Hanjina kaca mai kama riga

In fizgo mai hawa ni ban kula ba.


Tsiya na can mu je kan kadarko

Madaidaici in ce ba za mu hau ba.


In hau bisa kafaɗar bari na zauna

Kamar mahayin daɗai bai hauni shi ba.


Sukai ka'ida da Sale a kan kadarko

Sai yace "Haba Sale ba zan yadda kai ba.


Daɗai suka wantsala hakan kan ya ƙwace

Ashe ba Sale ne a cikin ruwa ba?


Ya bi shi ya bangaje ya buge yana ce

A zo a gani idan ban yada kai ba.


Malam Sale sai da ya tuɓe riga

Ya sa ka ga Sale har bai sha ruwa ba.


Ya tashi ya hau tudu keke ya bi shi

Da rigar Sale keke bai sako ba.


Su malam Sanda duk suka tarma keke

Da ban magana ya ce ba zai sako ba.


Ya ma rantse da jirgi har da mota

Ba za shi sako in ba a sa wuƙa ba.


Malam Sanda wai sun shirya da keke

Wai yana ƙaunarsa ba domin tsiya ba.


Ya ce haba malami kamarka

Ba zan iya yadda babban malami ba.


Izan dai za ka hauni ka tara riga

Da wando ba ka hau ni hawan isa ba.


Ya tashi hawa bai tattara ba

Ya fizgo malamin ba a jinjima ba.


Ya yasai nan da nan a tsakar gidansa

Cikin matansa tun ba a kai daɓe ba.


Yace Bari nai kure yashe ka malam

Dama ban kai ka bakin kasuwa ba.


Ba na son na yada mutum na kirki

Izan ba inda za ai dariya ba.


Da motsa ƙararrawarka da kama burki

Ba za su hana ni in jefar da kai ba.


Ya ce masa ba na ƙara hawanka keke

Ya ce masa ko adankiya ban kula ba.


Hawan da rashin hawan a gare ni ɗai ne

Ban ga abin da zai cutar dani ba.


Kamar tafiya ta sauri ko ta fizge

Ba ka je inda ka so nan da nan ba.


Izan ka zo ka hau ni ka ba ni iska

Na sha, ba inda ba zan je da kai ba.


Ashe ba mai hawa keke ya more

Izan ba wanda ya iya zanzaro ba.

Ɗaukowar:

Abbas Musa Jega
abbasmusajega750@gmail.com.
Ɗalibi A Sashen Harsunan Nijeriya Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments