Ticker

6/recent/ticker-posts

Waƙar Hijabin Gaskiya

Wannan wata tsohuwar waƙa ce fiye da shekara ashirin tun muna islamiyya ake yi wa ƴan makaranta ita, musamman ɗaliban da suka yi Malja'is Sunnah Islamiyya Sabon Gari Jega (Makarantar Ɗan'sule).

1. Ya Rabbana ya Rabbana ya Rabbana

Ya Rabbi ka taimaki mai hijabin gaskiya.


2. Bismil Ilahi Rahimi Sarkin nan guda

Na gode Allah mai dare mai sahiya.


3. Na roƙi Rabbi ya ban fusaha kamila

Zan tsara waƙa kan hijabin gaskiya.


4. Babban mayafi ne a kan riga ya zo

Ya dire a kan ƙasa babu siffar kwalliya.


5. Ba shafa jambaki turare tozali

Kayan ƙawa kaf ba a bayyana ko ɗaya.


6. Shi dai hijabi wajibi ne Rabbana

Ya aza shi a kan mata masoya gaskiya.


7. Sannan hijabin gaskiya in kula

Shi ne cikakke ba alamar kwalliya.


8. Najimin da bai wa mace hijab sai mu ce

Ya saɓa sunnah sai ya zo ya bi gaskiya.


9. Matar da ba ta son hijabi sai mu ce

Wannan khabisar ba ta layin gaskiya.


10. Ya ba ta shadda har atamfa ta haɗa

Leshi da kamfala wai don ta yi kwalliya.


11. Amma hijabi ko guda bai ba ta ba

Don ɗai rashin ilimi na kishin gaskiya.


12. Matar Duyusi ta yo ƙawa ta yo waje

Kai bar su ma haka kaiconsu kaico shi ya.


13. Mutabarrija mutazayyina mai ɗan gyale

Kaicon ki tuba ki sa hijabin gaskiya.


14. Babban abin sha'awa a ce ga ɗaliba

Ta tsara kanta cikin hijabin gaskiya.


15. Babban abin ƙyama a ce ga ɗaliba

Ta cokale kuma za ta ilimin gaskiya.


16. Ilimi na kirki Rabbana bai ba da shi

Gun wanda ke saɓa hanyar gaskiya.


17. La'ana ta Allah ta diro ka jahilai

Har malamai maƙiya hijabin gaskiya.


18. Sukar hijabi inda matan Muminai

Kufurun ku bar su kawai ku zo ku bi gaskiya.


19. Wata tai hijabi sai ta ɗebe tagguwa

Ta sa mayafi can ƙasan tai kwalliya.


20. Ibilis ya ja ta ya ce ta sanya rabin hijabi

Don ɗai a ce ta tara kayan kwalliya.


21. Ni dai wasiyyata ga matan Muminai

Su tsare hijabi don a san su da gaskiya.


22. Ahzabu sura ta azo dokar hijab

Ta ce Rasulu ya kai mu hanyar gaskiya.


23. Ƴaƴansa, matayensa, matan Muminai

Su tsare hijabi don a san su da gaskiya.


24. Mata ku tuna da Maryamu har Asiya

Aljanna za su shiga dalilin gaskiya.


25.bSannan ku lura da Wa'ila har Wahila

Wuta za su je don ƙin ɗabi'ar gaskiya.


26. Ƙat tamma nazmi hahuna ya ƴan'uwa

Na roƙi Allah gafararsa gaba ɗaya.


27. Ya Rabbana ya Rabbana ya Rabbana

Ya Rabbi ka taimaki mai hijabin gaskiya.

Ɗaukowar:

Abbas Musa Jega
abbasmusajega750@gmail.com.
Ɗalibi A Sashen Harsunan Nijeriya Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato.

Post a Comment

0 Comments