Ticker

6/recent/ticker-posts

Alƙalai - Ta Malam Khalid Imam

Ita soshal midiyan nan,
Su Fesbuk har Tiwita,
Ba abin da suke tuna min,
Sai hisabi ran ƙiyama.

Fesbuk na bani tsoro,
In ka yi yabo da zagi,
Tun bara a naka shafi,
Da kansa ya ke tuna ma.

Bai jin kunyarka shi sam,
Ko ko tsoro aboki,
Ranar na ke wayo wa,
Sai yai saurin tuna ma.

Ko ka mutu bai kula wa,
Ko kai mata da 'ya'ya,
Alheri ko tsiyarka,
Wallahi yana tuna ma.

Amma a hakan wasunmu,
Su ke ta saki na baki,
Hassadarsu ga ɗan uwansu,
Ba sa ɓoye ta Fesbuk.

Tabbas Fesbuk Tiwita,
Su Instagiram da Wasof,
Alƙalai ne gare ka,
Tun kafin ran ƙiyama.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments