Ticker

6/recent/ticker-posts

Tushiya - Ta Usman Balangu

(01) Tilas mu gode Jalla Hausawa daɗa,

Domin ko al'adun mu sun yi fice a faɗin duniya ba baya ba.

(02) Kaf a Afirka ina ya mu nai tambaya?

Mun kere kowa ba sa'a kaf duniya na bakwai muke kan cigaba.

(03) Mamaki a al'adun Bahaushe ya tuƙe,

Bukukuwa da kalankuwa da hawa na salla tuntuni ba baya ba.

(04) Takuttaha da biki na aure namu na,

Zane na suna Maulidi haka nan na Ƙur'ani buki ba a ƙi shi ba.

(05) Muke da tashe ga su wasan kokawa,

Shaɗi da dambe har da langa ga su tirna Hausa kau ba baya ba.

(06) Gargajiya sana'unmu tun tun tutuni,

Tafi ga Masaƙa ga Masunta ga Majema sassaƙa ba a bar mu ba.

(07) Marina da Wanzamanmu Dukawa daɗa,

Kau ga Manoma ga Maƙera har Mahauta har Maɗinka mun gaba.

(08) Riguna na Al'ada akwai mu da tsamiya,

Da bagobira girke da kwakwata ga ɓarage har da bulla kan gaba.

(09) Wandunanmu sun kere da kwai kamun-ƙafa,

Da tofi har da kwarjalle da fatari da buje Hausa ta yi awon gaba.

(10) Hulunanmu na Hausa ba tamkar ya su,

Ai tamkar dara ga zanna har da haɓar-kada da damanga ba.

(11) Rawunanmu kwai darke da harsa faktufi,

Da akoko ɗan sardauna ga lailai da ‘yan kura baza ko su ɓoyu ba.

(12) Kayan adon mu iri-iri ga tsakiya,

Munduwa da ma sarƙa da ɗankunne da murjani ƙarau ba baya ba.

(13) Bishiyin mu jingim ga su nan ko iri-iri,

Ɗinya da kanya ga su gawo kau da ma darbejiya ba a bar su ba.

(14) Ɓaure shirinya har da ma dai ɗorawa,

Kuka hano kisli gami da ararraɓi bishiyu ba a ɗara Hausa ba.

(15) Kaya na gun aikin gida ƙore akwai,

Akushi kuyafa ludayi da likidiri ga taskira ga ragaya ba baya ba.

(16) Kayan kiɗi gurmi garaya namu na,

Tambari da kotso ga su jauje kai da taushi gun kiɗi ba baya ba.

(17) Tafi ga su shantu ga su molo namu na,

Haka ga kalangu kukuma turu da goge gun kiɗi ba a bar mu ba.

(18) Kaya na busa ga sarewa ta mu ta,

Da ƙaho da algaita da kakaki a busa bam mu bar su a yase ba.

(19) Makaɗa na al'ada da dama an sani,

Shata da Ɗanƙwairo Narambaɗa Jankiɗi Sarki na taushi kaji ba.

(20) Ga Ɗan'anace Sa'idu Faru haɗa duka,

Gambu mijin Kulu har da Maidaji Haruna Uji ka sa su akan gaba.

(21) Ga nan takobi ga su kunkelen fwaɗa,

Sannan da sango har da mashi kwalkwali sulke na yaƙi kun ji ba.

(22) Ɗamara ta yaƙi har da ma kansakali,

Ga gariyo adda da ma fa barandami kibiyar kwari da baka haba!

(23) Da majaujawa kana da ma takunkumi,

Ga sasari sannan da sarƙa ga mari ga garkuwa babu fargaba.

(24) Na yo salatai gun Rasulu da Alihi,

Asahabu sanyo Rabbana Usman Bulangu ba za na kai ya irinsu ba.

(25) Mudu na waƙar sai ka auna ga shi nan,

Mustaf'ilun Mustaf'ilun Mutafa'ilun,

Mustaf'ilun Mustaf'ilun Mustaf'ilun Mutafa'ilun Mutafa'ilun.

 TAMAT

Laraba, 17 ga Mayu, 2023.


USMAN IBRAHIM BULANGU

09064862386

Post a Comment

0 Comments