Ticker

6/recent/ticker-posts

Mene Ne Hukuncin Mai Janabar Da Ya Karanta Alƙur'ani?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Allah ya kara wa malam lafiya ameen. Malam menene hukuncin Wanda yakaranta wasu surori daga cikin alƙur'ani alhalin yana cikin janaba wato bai tsarkake jikin sa ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salám, Mafi yawan malaman Fiƙhu daga Mazhabobin nan huɗu sun tafi a kan haramcin karanta Alƙur'ani ga mai janaba ko da kuwa da ka ne.

Imamut Tirmizhiy ya bayyana cewe: "Wannan fahimtar ita ce maganar mafi yawan ma'abota ilimi daga cikin Sahabbai da Tabi'ai, da waɗanda suka biyo bayansu, kamar su Sufyanut Thauriy, da Ibnul Mubárak, da Assháfi'iy, da Ahmad da Ishaƙ". Sunanut Tirmizhiy (1/195).

Haka nan Alkásániy ya ce: "Ba ya halasta ga mai janaba ya yi karatun Alƙur'ani a wurin gamayyar malamai". Badá'i'us Saná'i'i (1/37).

Shaikhul Islam Ibn Taimiyya ya ce: "Haka nan mai janaba ba zai karanta Alƙur'ani ba a fahimtar mafi yawan malaman mazhabobin Fiƙhu guda huɗu, da ma wasunsu, kamar yadda Sunnah ta yi nuni a kan haka".

Duba Majmú'u Fataawá na Ibn Taimiyya (17/12).

Saboda haka ‘yar uwa ba ya halasta ga mai janaba ya karanta Alƙur'ani har sai ya yi tsarki, wanda kuma ya yi hakan ya yi kuskure a bisa fahimtar mafi yawan malamai. Kuma wannan ita ce Fatawar da Lajna suka bayar a mujallad na biyar shafi na 429.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments