Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarkin Musulmi Attahiru Da Hijirarsa Zuwa Ƙasar Gabas Da Kuma Yaƙi Na Ƙarshe A Ƙasar Sakkwato (Yaƙin Giginya)

Sarkin Musulmi Attahiru Da Hijirarsa Zuwa Ƙasar Gabas Da Kuma Yaƙi Na Ƙarshe A Ƙasar Sakkwato (Yaƙin Giginya)

A Safiyar 15 Ga Watan March 1903 Turawan Mulkin Mallaka Bayan Kare Manyan Daulolin Kasar Hausa Sun Dunfaro Kasar Sakkwato Domin Yakin Daular Usmaniyya.

Sarkin Musulmi Na Wannan Lokacin Wato Muhammadu Attahiru Dan SM Ahmadu Dan SM Abu Bakr SM Atiku Dan Shehu Uthmanu Dan'hodiyo Ya Fita Da Rundunar Dakaru Mutum 6000 Wadda Aka Kasata Gida Uku

1. Karkashin Jagorancin SM Attahiru

2. Karkashin Jagorancin Sarkin Ra6a Ibraahimu

3. Karkashin Jagorancin Marafa Muhammadu Mai Turare.

Latton Da Yakin Ya Kaure Tsakani'n Jama'ar Musulmi Da Kahurawa An Kashe Mutum 100 Cikin Musulmaii Amma Batare Da An Kashe Kowa Daga Turawan Ba Dalili Kuwa Shine Suna Da Makamaii Wato(Bindiga) Wadda Su Mutan Kasa'r Sakkwato Na Wannan Lokacin Basuda Wadannan Makaman.

Daga Ciki'n Wadanda Sukayi Rakkiya Wa SM Attahiru Akwaii

Mallan Ubandoma, Babban Alkalin Aadamawa Mudi Abdu,. Ahmadu Dan Modi Maji Dan Magaji, Dan Magaji, Dan Waziri,Sarkin Kwanni Da Madaki.

 

Daga Ciki'n Talakawa Kuwa Mutum 10,000 Sunkabi SM Zuwa Hijira Kasar Gabas.

Saboda Haka Sai Yazamana Gabadaii Kasa'r Sakkwato Turawan Suka Mamayeta Karkashin Jagorancin "Lord Lugard"  


Daga Ciki'n Wadanda Basubi SM Attahiru Ga Wannan Hijarar Ba Akwaii

1. Wazirin Sakkwato (Muhammadu Bukhari)

2. Galadiman Sakkwato

3. Sarkin Yaki

4. Magajin Gari

Sun Zabi Suyi Mu'amala Da Turawa Kuma Sun Zauna Sun Sake Zaben Sabon SM

Bayan Turawan Sun Karbi Mulki Duk Wani Babban Nadin Da Za'ayi Saida Yawunsu.

Duk Da Cewa Kasa'r Sakkwato Koko Ince Daular Usmaniyya Daulace Ta Musulunci Mai Bin Tafarkin Ma'aikin Àllah (S.A.W), Amma Lord Lugard Da Wasu Cikin Manyan Masu Fada Aji Sun Canza Wannan Gini Da Shehu Dan'hodiyo, Mamman Ballo Da Mallan Abdullahin Gwandu

Suka Aza Mutane Akaii.

Daga Watan March Zuwa July Na 1903 SM Attahiru Ya Aika Sako Ga Sassan Daular Kamar Kano, Borno, Aadamawa Yanayin Allah Wadaii Da Sakin Koyarwa'r Addinin Allah Da Sukayi Sunkabi Koyarwa'r Nasaara Ya Kara Da Cewa Zayyi Hijira Zuwa Kasa'r Gabas. Kuma Alhamdulillah Mutane Da Yawa Sun Amsa Kiransa

Shine Shehu Dan'hodiyo Yake Cewa

"Izan  Sarkin Musulmi Zashi Makka"

"Akayi Muna Kira Amushirya Kaya"

Latton Da SM Attahiru Yakaii Kasar Kwatarkwashi 31 Ga March Sarkin Katsina Na Wannan Lokacin Ya Aika Masa Wasika Yana Masa Tanbihi Aka'n Yana Kusa Da Lord Lugard Da Runduna Tasa Don Haka Yayi Kaura Ya Kuma Aika Masa Da Kayan Abinci,Dabbobi Da Tufafi.

Wannan Irin Taimako Da Sarki'n Katsina Ya Ba SM Attahiru Duk Manyan Daulolin Uthmaniyya Sun Bada Kwatankwacinsa Amma A Boye Saboda Tsoron Abinda Ka Iya Biyo Baya Daga Lord Lugard.

Shi Yassa Shehu Dan'hodiyo Yake Cewa

"Zama Kasan Zama Domin Lalura"

"Akwaii Guzuri Ku Basu Ku Samu Lada"

Ma'ana 

Wadanda Yazamana Basu Samu Damar Wannan Hijarar Ba Su Taimakama SM Don Su Samu Lada 

SM Attahiru Ya Cigaba Da Kutsawa Cikin Birane  Da Kauyukka Yana Kiransu Da Su Bishi Suyi Hijira Wasu Sun Bishi Wasu Kuma Sun Bada Taimako Na Kayan Abinci, Dabbobi Da Tufafi

Daga

✍️ NAZIR KABIR HALI (MALLAN)

Post a Comment

0 Comments