Ticker

6/recent/ticker-posts

Sarautar Ubangiji

 1-

Da sunan Ubangiji,

Da dake bamu agaji,

Ya yi komai aji-aji,

Da tsuntsu da fiffike.

2-

Suradhal Lazi ya ke,

Da an bi Shi an fake,

Halittarmu Shi yake,

A koman daban Ya ke.

 

3-

Yana ci da tsurruka,

Da ƙwari a tsaunika,

Da yai kum! da an haka,

A bauta ga shi mu ke.

 

4-

Bai haifa ba Ƙadiran,

Muridan mubasshiran,

Gwani anta ƙalikhan,

Fiyayye da Kai na ke.

 

5-

Shi ke bamu lafiya,

Idan babu tun jiya,

Shi ke kare duniya,

A koma ina ta ke.

 

6-

Shi ke kai mutum sama,

Ya koro shi ya  gama,

Ba a faɗar ka ka gama,

Ka san Shi daban Ya ke.

 

7-

Kuna zaune lafiya,

Ya watso hajijiya,

Take zaga Nahiya,

Gidajen zuba su ke.

 

8-

Da lotonka ya wuce,

A rannan da ka mace,

Za ka zama kamar ice,

In sharholiya ka ke.

 

9-

Sarauta ga Shi ta ke,

In ya baka ka sake,

Bala'an a nan su ke,

Don Ya baka ka sake.

 

10-

Wanda Ya ƙagi duniya,

China ƙasar ltaliya,

Ghana da Y'an Nijeriya,

Dukka a ƙarƙashi mu ke?

 

11-

Shi Allahu Ya sani,

Don baya biɗar tuni,

Komai namu Ya sani,

Ka bar wai ina Ya ke?

 

12-

Ka kai kanka lahira,

Ka zo nan ka sha jira,

Da kwananka yai kira,

Da ka san ina Ya ke!.

 

13-

Mata ban da ɗan cikin,

Ta dawo ga Maliki,

A rannan abin cikin,

Zai fita ko ina take.

 

14-

Zai kuma rayu duniya,

Ya lalleƙa Nahiya,

Ya je Umma'ahiya,

Tunaninsa ma ake.

 

15-

Ku dudduba dazuka,

Duwatsu da tsaunuka,

Halittu a ramuka,

Faɗar Rabbana su ke.

 

16-

Kana kwance ka mutu,

A na wane ya mutu,

Su lamin da Saratun,

Ba su kiran ina ka ke!

 

17-

Ka fita fes da sallama,

Ka dawo kamar rama,

Kai hatsarin arangama,

Ba ka sanin ina ka ke?

 

18-

Jari Ya baka mai yawa,

Kullum sui ta hauhawa,

Randa ya sake waiwaya,

Baka sanin  ina su ke!

 

19-

Da can kun ta'azzara,

Yanzu ko kun tagayyara,

Don haka sai ku ankara,

Yau damarku ya take?

 

20-

Allah gani na tsaya,

Kangala ne na tambaya,

Zan wa'azi da ɗauraya,

Kan ikonKa ya ka ke.

 

Marubuci:-

Abdullahi Lawan Kangala

 

Haƙƙin Mallaka:

Phone:- +2348033815276

KANGALA GLOBAL AWARENESS VIA MEDIA

Post a Comment

0 Comments