1.
Bugun zuciya
mai tura so da ƙauna
kowanne sashe.
2.
Budurwata ce
ta ce sai da ta tace
sannan ta d'au ni.
3.
Kun ga mak'iyi
na cike da 6acin rai
don ya sha kaye.
4.
To ba ta sonka.
Ya za ka yi da k'auna
ta yi fiffike.
5.
Duk jan idonka
ko bak'in cikinka ni
ne dai za6inta.
6.
An ce ka fito
ka kasa. Turo Su'Ab
nan ma ka gaza.
7.
Kullum sai k'arya!
Kai fes da kayan aro
da ba sa ado.
8.
Wai kai nan wane.
Alhali duk an gane
Hankaka kake.
9.
To ta k'i wayon
Jeka ka yi ta zambon
duk fa a banza.
10.
In tunaninka
mata du wawaye ne
to banda ita.
11.
Je nemi wata
Afiruwa daidai kai
K'warya bi k'warya.
12.
Kid'an tambura
da algaitu sai Sar'ki
ba na kowa ba.
13.
Tai mini Bai'a
Ta d'oran kambina Tajh
Mai Sarautarta.
14.
Ka gatsi laya
har da tauna su hanta
Jikon ya kife.
15.
Yashin jidali
Yara ba sa wasa kai
Sai dai a kwashe.
16.
Mai tada gari
Ya hadarin duwatsu
Mai kar zuciya.
17.
Ka kira bara'
Ta ja maka "Lahaula..."
Yaro da 'Kili.
18.
Mu kuwa bajau
Shimfid'a har matasu
kore ga taushi.
19.
Ni'imatulLaah
'Yan biyu su goma sha
Kowanne Khalid.
20.
Sannu Dutsen Gwal
Ka wuce awon wargi
A da da yanzu.
21.
Mace ta gari
alJannah ce a dunya
Balle a Akhir'.
From the Archive of:
Malam Muhammad Tajajjini Tijjani
Imel: mmtijjani@gmail.com
Lambar Waya: +2348067062960
©2023 Tijjani M. M.
0 Comments
Post your comment or ask a question.