Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Matarsa Tana Cikin Idda

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Miji ne ya saki matarsa saki ɗaya, amma sai yace ta zauna a gidansa ta yi iddah, to tana iddar kuma ya je mata kamar sau uku yana Saduwa da ita sai daga baya ya ga ta yi jini uku sai ya ce wai iddarta ta kare zata iya tafiya gida. to ya ya wannan mu'amalar da ya yi da ita akwai aure ko ya lalace sai an sake sabon daurin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan mutum ya saki matarsa, kuma wannan sakin ya kasance shi ne na farko ko na biyu to bata fita daga idda ba, idan ya so zai iya maido ta da furuci, misali ya ce na maidoki ko na cigaba da rikonki. Ko ya maidata ta hanyar wani aiki da yake nufin mayarwa, kamar ya kusanceta da niyyar mayarwa to mayarwar ta yi.

Iddar macen datake haila shi ne: Al'ada uku (jini uku) idan ta samu tsarki daga wannan jini ukun ta yi wanka, to tagama iddarta.

Iddar macen da bata haila saboda yarinta kota daina hailar, wata uku ne za ta yi.

Iddar mai ciki kuwa shi ne ta haife abinda ke cikinta, abinda ya gudana na jima'i bayan wannan aikin haramun ne.

Wajibi ne Wannan mijin yatuba zuwaga Allah maɗaukakin sarki akan afkawa jima'in dayayi tare da ke, bisa rashin kudurce komai na dawo dake ba, kuma ya zama wajibi Ku sake daura wani auren da Sharuddansa na waliyyi da shedu da siga da sadaƙi idan kowannenku ya na kwadayin hakan.

Ba ya halatta a gareshi ya sake kusantar ki, har sai ansake daura muku sabon Aure.

Saboda haka wannan kusantarki dayayi ba tare da ƙudurce yai maidake ta sigogin da malamai suka tattauna wanda suke nuna mutum ya dawo da matarsa ba, haramun ne yanzu a gare shi yasake yi miki duk wani abu daya halatta tsakanin miji da matarsa har sai an daura muku sabon Aure da sadaki da shaidu da waliyyi.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments