Sanya Hoton Gawa Ko Mara Lafiya A Kafafen Sada Zumunta

    Ina yi wa kowa fatan alheri.

    Haƙiƙa ina cike da damuwa da ƙyamar ɗabi'ar da wasu suke da ita na sanya hoton gawa ko wani mara lafiya musamman a kafafen sada zumunta. Mafi yawan masu yin hakan suna yi ne da nufin neman addu'ar rahama ga mamaci ko neman lafiya ga majinyaci.

    Da dama daga cikin hotunan da akan sanya za ka samu ba su da kyawun gani. Idan mamaci ne za ka gan shi a yanayi mai firgitarwa, wani baki a wangame, tsiraicinsa a waje, ko kuma a cikin likafani wanda yana firgita wasu idan sun gani. Wani abin takaici kuma shi ne wasu za ka samu har a maƙabarta a dai dai lokacin da ake sanya gawar a cikin ƙabari, ba abin da suke yi sai ƙoƙarin ɗaukar hotonta. Ko amfanin me zai yi musu? Oho!

    Marasa lafiya kuwa akan É—auki hotonsu a halin jinya. Wani yana kan gadon asibiti, ya rame, ya jeme, ga shi an sanya masa robar hanci ko ta fitsari ko kuma cikin bandeji. Idan kuwa hatsari ya yi, sai ka ga an sanya hotonsa face-face da jini babu kyawun gani. Duka waÉ—annan ban san amfaninsu ba.

    Ya kamata masu aikata irin wannan abu su lura cewa:

    1. Shin idan su ne a wannan halin, za su so a yaÉ—a hotonsu a halin jinya ko gawarsu bayan sun mutu?

    2. Wane ne zai so a yi wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa haka?

    3. Wane ne zai so a yi wa matarsa irin wannan tereren?

    4. Idan addu'a ake buƙata, dole ne sai an sanya hoton mutum?

    5. Wace riba za ka samu idan ka yaÉ—a hoton mutum a haka?

    6. Ba ka gudun É“ata aikinka da riya?

    7. Mene ne amfanin hakan da ka yi.

    Na tabbata wannan ɗabi'a ta saɓawa lafiyayyen hankali, haka kuma ta ci karo da manufar Shari'a ta kare mutuncin musulmi.

    Ina yi wa masu irin wannan halin nasiha da cewa, su ji tsoron Allah, su ƙauracewa wannan hali mara amfani. Su duba maslahar tsare mutuncin wanda suka yi haka.

    Idan kuma buƙata ta dole ta sa sai an yi hakan, wataƙila domin neman gudummawa ko cigiya, to sai a yi ƙoƙarin ɗaukar matakan da za su kare mutuncin wanda hakan ya shafa.

    Muna roƙon Allah ya datar da mu a dukkan lamura. Marasa lafiyar cikinmu, muna roƙon Allah ya ba su lafiya. Allah ya ji ƙan magabatanmu. Allah ya sa mu yi kyakkyawan ƙarshe.

    Naku a addini.

    By:

    Imrana Hamza Tsugugi
    +2347039784456

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.