𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Yaya Matsayin Alƙunutu Da ake Karantawa Asallar Asubahi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Asalin Alƙunutu asallar asuba
malamai sun yi saɓani a kansa akwai waɗanda suke ganin shar'antuwarsa kamar
malikiyyah da shafi'iyyah, akwai waɗanda basa ganin shar'antuwarsa kamar
Hanafiyyah da Hanabila.
Ibnu ƙudama rahimahullah a cikin
Almugni (1/449) Ya ce: Ba sunnah bane alƙunutu asallar asuba ko watanta daka
cikin salloli, inba wutiriba, haka Assauri yace da Abu hanifa, haka aka ruwaito
daka ibnu Abbas, da Abdullahi dan Umar da Ibnu mas'ud da Abul dar-daa'i.
Malik da Abi laila da hasan bin
salih da shafi'i sukace: Sunnah ne yin alƙunutu asallar asuba adukkanin za munnah
domin Anas ya ce: (Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam baigushe ba yana alƙunutu
asallar asuba har yabar duniya) Imamu Ahmad a cikin Musnad ɗinsa.
Umar yakasance yana Alƙunutu
agaban sahabbai da wasunsu.
da Abun da aka ruwaito Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam ya yi alƙunutu tsawon wata guda akan wasu larabawa
rayayyu sannan yadena. Muslim.
Abu huraira yaruwaito irin wannan
hadisin daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam,
(Annabi Sallallahu Alaihi
wasallam yakasance baya alƙunutu asallar asuba saidai idan zai yiwa wasu mutane
addu'a ta alkhairi, kozai musu addu'a mummuna.)
Alƙunutun Umar yakasance lokacin
saukar musibu domin mafiya yawan ruwayoyi sunzo akan baya alƙunutu, jama'a
dayawa sunruwaito haka daka gareshi, wannan yake nuna baya alƙunutu sai
alokacin saukar musiba. Mausu'ah fiƙ-hiyyah (34/58).
Tare dacewa magana mairinjaye ita
ce: Baya halatta yin alƙuntu asallar asuba ko da yaushe saidai idan masifa
tasauka, Saidai babu laifi dankayi sallah abayan wanda yake alƙunutun asallar
asuba ɗin, dayin Ameen a addur'asa.
Shaikul Islam ibnu taimiyyah
rahimahullah ya ce: Idan mamu yabi limamin dayake alƙunutu asallar asuba ko
sallar wutiri zai yi ƙunuti tare dashi, yana alƙunutunne kafin ruku'u ko bayan
ruku'u. idan baya alƙunuti ba zai yi ba.
Koda liman yana ganin
Mustahabbancin wani abu, mamu kuma baya ganin hakan sai ya barshi dan samun
haduwar kai da hadewa yakyauta, Maj-mu'u fatawa (22/ 268).
Dan haka dai lazimtar yin alƙunutu
ko da yaushe asallar asuba ba sunnah bane, saidai idan wata matsala ta tunkaro
musulmi ko wani bala'i sai aita alƙunutu har sai Allah yakau da wannan
matsalar.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.