Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallah Da Tufafi Mai Najasa

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Tufafin Mutum Yasamu Najasa Kuma Bai Samu Ruwanda Zai Wanke Ba, Bashi Dawani Tufar Dazayi Sallah Dashi Yaya Zai yi?.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Sallah bata ingantuwa da tufa mai najasa, Mutum zai iya sallah ne da tufafi masu tsarki, saboda faɗin Allah madaukakin sarki:

(ﻭَﺛِﻴَﺎﺑَﻚَ ﻓَﻄَﻬِّﺮْ ‏) ﺍﻟﻤﺪﺛﺮ 4

Ka tsarkake tufafinka.

Wata mata ta zo wajan Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ta ce: Jinin haila yana taɓa tufafin wata daka cikinmu yaya za ta yi? Ya ce: Tawankeshi daruwa Tamatse shi sannan Tayarfe ruwan, sannan saitayi sallah da tufafin.

Bukhari (227) da Muslim (291)

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceta data tsarkake tufar kafin tai sallah da ita.

Idan najasa tasamu tufafin mutuminda bashi da wani tufafin dazai sallah sai mai najasar kawai, baya wuce halayae uku

1- Zai iya wanke wajanda najasar datake jikin tufafin yai sallah dashi, kamar najasar ajikin hannun riga ko gefen karshen riga take, wajibi ne wanketa yai sallah datufafin, domin yanada ikon sallah datufafi maitsarki babu uzuri a kansa idan yai sallah danajasa.

2- Zai iya cire tufafin ba tare da Al'aurarsa tabayyana ba, kamar idan yanasa wani kayan daka ciki wanda yake rufe al'aurarsa (gajeran wando singileti, sikel diras) wajibi ne yacire tufar yai sallah damai tsarki, saboda haka ne Annabi sallallahu Alaihi wasalla yacire takalminsa mai najasa ajikinsa yana cikin sallah lokacinda jibirilu Alaihissalamu yasanar dashi akwai najasa ajikinsu.

Abu dauda (650) Albani ya ingnatashi a cikin sahihu Abu dauda

3- Bashi da wani tufafin mai tsarki dazai sallah dashi kuma ba zai iya kawarda najasar ba, magana ingantacciya cikin zantukan malamai shi ne zai sallah dawannan tufar mai najasar, saboda ya zama mai uzuri, kuma sallarsa ingnatacciyace ba zai sake sallar ba bayan yayita da tufafin.

Shaikul Islma ibnu taimiyyah Allah yajikansa ya ce: Wanda baisamu tufafi ba sai masu najasa kaɗai? Wasu malamai sukace: ya yi sallah tsirara, wasu sukace: yai sallah datufafin Amma yasake sallar, wasu sukace: Yai sallar dasu haka ba zai sake sallar ba, wannan shi ne ingantaccen zance cikin zantukan malamai domin Allah bai umarci bawa ya yi sallar farillah sau biyu ba, saidai idan baiyi wajibinda aka dora masaba tunfarko, kamar yai sallah babu nutsuwa zai sake sallah kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya Umarci wanda yai sallah babu nutsuwa a cikinta ya ce: (Koma ka yi sallah danbakayi sallah ba, haka wanda yamanta tsarki yai sallah babu alwala, zai sake sallah kamar yanda Annabi sallallahu Alaihi ya umarci mai lam'a akafarsa bai wankeba yasake alwala da sallah, Amma wanda ya aikata abun da aka kaddara masa gwar-gwadon ikonsa Allah madaukakin sarki ya ce:

 ﻓَﺎﺗَّﻘُﻮﺍ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣَﺎ ﺍﺳْﺘَﻄَﻌْﺘُﻢْ ‏.

Kuji tsoran Allah gwar-gwadon ikonku.

Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce:(Abun da na Umarceku kuzo dashi gwar-gwadon Abun da zaku iya).

Majmu'u fatawa (22/ 34-35)

Saboda haka zai yi sallah datufafinda suke danajasar babu komai a kansa domin anmasa uzuri kuma ba zai sake sallar ba, bayan uzurin yagushe daka kansa.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.