Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Kalmomin Fannu

A CikinWannan Rana: (A cikin wasar A CikinWannan Rana) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa tsakanin rukunin masu wasa guda biyu. Na dandali ne, sannan yana tafiya da waƙa.

A Fiffigi Zogale: (A cikin wasar A Fiffigi Zogale): Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na gaɗa da ke ɗauke da waƙa mai nuna halayyar matan aure zuwa ga wasu mutane daga cikin danginsu da dangin mazajensu da kuma kishiya da danginta.

A Fim-Fim-Fim: (A cikin wasar A Fim-Fim-Fim) Ɗaya daga cikin nau’ukan wasannin mata na dandali da suke tafiya da waƙa da tafi.

A  Sha Ruwa: (A cikin wasar A Sha Ruwa) Wasan tashe ne na mata da ke ɗauke da waƙa.

A  Sha Ruwan Tsuntsaye: (A cikin wasar A Sha Ruwan Tsuntsaye) Wasa ne da yara biyu ke jeruwa sannan su mayar da hannuwansu baya tare da sarƙafa yatsun hannuwan nasu. Wani yaron kuma zai hau bisa hannuwan nasu da ƙafafunsa tare da dafa kafaɗunsu. Za su riƙa yawo suna waƙa yayin da yake ɗangalafe.

Afajana: (A cikin wasar Afajana) Wasan yara maza da suke aje riguna, sannan sarki da turke su tsaya daidai wurin da za a ɗauki rigunan. Sauran yara za su riƙa ƙoƙarin ɗaukar rigunan ba tare da sarki ya taɓa su ba. Duk wanda ya ɗauki rigarsa, zai riƙa dukan sarki da ita.

Afurka-Afurka: (A cikin wasar Afurka-Afurka) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa.

Aika: (A cikin wasar Sabis) duba aike.

Aike: (A cikin wasar Sabis) yayin da ɗan wasa ya jambaɗi sabis da ƙarfi ƙwarai yadda har ta huce gabaɗaya abokan karawarsu, to ya aika abokan karawar.

Ajiye Sanda: (A cikin wasar sabis) 1: Yayin da wani ya shiga gidan abokan karawarsa da niyyar ya buga sabis, za su yi saurin furta wannan furuci kafin ya furta eskus, idan har sun riga shi, to abin da ya yi ya zama sata. Misali: Sun ambaci ~ saboda haka Musa ya yi sata. 2: Hukuncin da ake yi wa wanda ya yi sata. Zai ajiye sandansa a gidan abokan karawa sannan ya fita waje na tsawon wani lokacin da aka ƙayyade masa, kafin ya dawo ya ɗauki sandar domin ci gaba da wasa.

Alhaji: (A cikin wasar Sai Ka Yi Rawa A Nan) Sunan yaro ko yarinyar da ya/ta yi shigar dattijo yayin tashen.

Alhajin Ƙauye: (A cikin wasar Alhajin Ƙauye) 1: Wasar tashe ta yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar dattawa ya rataya jaka ya kuma riƙa dogara sanda. Wasan yana tafiya da waƙar da ke nuna cewa, wannan mai shigar dattawa Alhaji ne daga ƙauye wanda ya yi azumi zai je gida ga shi ba shi da kuɗin mota. 2: Sunan da ake kiran yaron da ya yi shigar dattawa yayin wasan.

Aliyar Gwangola: (A cikin wasar O Aliyu) Sunan wadda mijinta ya yi tafiya ya bar ta gida na tsawon lokaci a cikin wasan.

Allah Reni: (A cikin wasar Allah Reni) Wasan dandali na yara maza wanda ake rufe wa yaro guda ido. Sauran masu wasa za su riƙa tsallake shi ɗaya bayan ɗaya. Ga duk lokacin da aka tsallake za a bukaci ya bayyana sunan wanda ya tsallake shi. Idan ya bayyana daidai, wanda aka bayyana ne zai zauna a rufe masa idanu.

Allah Ya Ba Da Sa’a: Furucin da ake yi wa masu tashe a matsayin sallama yayin da ba za a ba su komai ba.

Allah Ya Ba Mu Ruwa: (A cikin wasar Allah Ya Ba Mu Ruwa) Wasar yara maza da mata da ake gudanarwa yayin da hadari ya taso tare da alamun ruwan sama.

Allazi Wahidun: (A cikin wasar Allazi Wahidun) Wasa ne na yara maza wanda ake amfani da takalmi a riƙa bugun ƙwallon goruba zuwa jikin abokan wasa. Duk wanda ƙwallon goruba ya taɓa shi, to zai sha duka.

Allazi: (A cikin wasar Allazi Wahidun) Suna ne da ake kiran duk wanda ƙwallon goruba ya taɓa ƙafarsa yayin da ake wasa.

Alo Na Taro Na Tattaro: (A cikin wasar Alo Na Taro Na Tattaro) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa, inda mai rerawa ke ambaton sunayen ƙawaye da ‘yan’uwanta.

Amali Kande: (A cikin wasar Amali Kande) Wasan dandali na yara mata da ke ɗauke da waƙa mai jan hankali game da auren dole.

Aminun: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Arbana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na biyar a wasan babunna.

Aro: (A cikin wasar Guro) Yayin da ɗaya daga cikin masu wasan guro ya bayar da gida ko gidaje ga wani daban domin ya yi tafiya da su da nufin idan wanda aka ba wa ya jawo wasu gidajen zai miyar wa wanda ya ba shi abinsa, to an yi aro ke nan.

Artabu: (A cikin wasar langa) daidai da gwabza.

Ashobe: Ɗinka kaya iri ɗaya da ake yi (A cikin wasar musamman mata) yayin bukin aure ko na haihuwa.

Audu: (A cikin wasar Rabi Da Audu) Sunan mai yin shigar maza a cikin tashe; wadda kuma ke kasancewa mijin Rabi.

Ayye Mama: (A cikin wasar Ayye Mama) Ɗaya daga cikin wasannnin da ake gudanarwa yayin kai amarya. Yana ɗauke da waƙar bankwana ga amarya.

Ayye Rashidalle: (A cikin wasar Ayye Rashidalle) Wasan yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai faɗakarwa game da tsabta.

Ba ‘yar Zubel Ba: (A cikin wasar Babunna) Idan wasa ba ‘yar zubel ba ce, wacce aka ƙwace a arbana ko wani gaɓa na kaɗin wan tu fayif za ta ci gaba daga wurin da aka ƙwace ta idan yin ta ya zagayo.

Ba Dela Ba Kande: (A cikin wasar Ba Dela Ba Kande) Wasan dandali na yara mata da ke ƙunshe da waƙa mai nuna ɗarsashin zuciyarsu.

Ba Ga Shi Ba!: (A cikin wasar Babunna) Furucin da wadda ta ci nasararojo ke yi na nuna, da ma ita ke da gaskiya.

Ba Kya Ci Ba: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Furucin da ’yan wasa ke yi na nuna, kura ba za ta kama ko ɗaya daga cikinsu ba.

Ba Mu Kuɗinmu: (A cikin wasar Ba Mu Kuɗinmu) Wasan tashe na yara maza da ake goya wa ɗaya daga cikinsu matashin kai a baya, sannan su riƙa dukansa a wurin tashe da sunan ya ci musu bashin doya, shekara guda bai biya ba.

Ba Mu Saya Ba: (A cikin wasar Sabis) Furucin da abokan karawar gidan da ke ba da sabis ke yi da ke nuna cewa ba su aminta da sabis da aka ba su ba.

Ba Ta Gagarel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furucin da ake yi domin a nuna cewa, dokar wasan ba ta ba da dammar gagarel ba. Saboda haka, wadda ta yi gagarel ta faɗi kai tsaye.

Ba Ta Jira: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake yi domin a nuna cewa, dokar gasar guro ta hana jira. Saboda haka, dole ne mai tafiya ya fara ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Ba Ta Masar Baba ne: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furucin da ke nuna dokar wasan ba ta ƙunshi masar baba ne ba.

Ba Ta Ƙirge: (A cikin wasar Guro) Furuci ne da ake yi kafin a fara wasa domin nuna cewa, dokar wasan ta hana ƙirge kafin tafiya.

Ba Ta Ƙonewa: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake yi domin nuna cewa, dokar wasa ta ba da damar mai wasa ya ɗebe haihuwarsa ko da ta ƙone.

Ba Ta Sa Baki: (A cikin wasar girjim/Guro/Uku Saɓi/Siri-Santa) Furuci da ke nuna cewa, dokar wasa ta hana sa baki a wasan da ake gudanarwa.

Ba Ta Satar Gaba: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Dokar wasa inda mai wasan da ta yi satar gaba ta faɗi.

Ba Ta Sizin: (A cikin wasar girjim) Furucin da ake yi domin nuna cewa, dokar wasan a wannan lokaci ta ba da dama a yi sizin.

Ba Za Ku Ga Tafiyar ’yata Ba: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar ’yata Ba) Wasan yara maza da ya shafi ɓoye tsakuwa a cikin ƙasa tare da buƙatar abokin wasa ya nuna wurin da aka ɓoye.

Wandara a Sha Maganin Ƙaba: (A cikin wasar Wandara a Sha Maganin Ƙaba) Wasan tashe na manya maza inda ɗaya daga ciki ke shigar dattawa sannan ya rataya abu cikin riga a matsayin gwaiwa/ƙaba.

Baba Mai Gadi: (A cikin wasar Baba Mai Gadi) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikin yaran ke shigar tsofi ya kuma riƙe sanda. Zai riƙa rawa yayin da sauran yara ke tambayarsa cikin waƙa ko rawar coko zai yi? Shi kuwa zai riƙa ba da amsa da cewa masallaci zai je, kada kuma su sa shi ya haukace. 2: Sunan yaron da ya yi shigar tsofi yayin wasa.

Baba: (A cikin wasar Ba Mu Kuɗinmu) Duk wani mutum da ka iske a wurin tashe.

Baba: (A cikin wasar Wandara a Sha Maganin Ƙaba) Wanda ke shigar dattijo mai ƙaba yayin tashen.

Baba: (A cikin wasar Na Ci Na Kasa Tashi) Wanda ake sanya wa tsummokara cikin riga yayin wasa.

Baban Dudu Zai Gudu: (A cikin wasar Baban Dudu Zai Gudu) Wasan tashe na yara maza inda Baban Dudu ke yin shigar tsofi ya kuma ɗauko faggon kaya. Waƙar wasan na nuna cewa, Baban Dudu zai gudu ne saboda auren Dudu ya matso kuma ba shi da kuɗin aurar da ita.

Baban Dudu: (A cikin wasar Baban Dudu Zai Gudu) Yaron da ke shigar tsofi a cikin wasan.

Babana Ya Sami Min Ƙwallo: (A cikin wasar Babana Ya Saya Min Ƙwallo) Wasan yara maza ne masu ƙarancin shekaru. Yana ɗaya daga cikin wasannin da ake yi da ƙasa.

Babu: (A cikin wasar Jini Da Jini): Furucin da masu wasa ke yi yayin da aka ambaci sunan abin da ba shi da jini, kamar akwati ko randa da sauransu.

Babunna: (A cikin wasar Babunna) 1: Wasa ne mai sigar Ɗan Balum-balum da ake tsalle-tsalle da tafi da kuma buɗe ƙafa da tsukewa. Sai dai waƙar da ake yi ciki ta bambanta da na Ɗan Balum-balum. 2: Kaɗin farko na wasan babunna a cikin kowace randa.

Bafade: (A cikin wasar ’Yar Ganel) Wanda ke ɗauko saƙo daga sarki zuwa ga ‘yan wasa yayin da ake wasan.

Baji: (A cikin wasar Carafke) Barbaza ’ya’ya a ƙasa yayin fara carafke.

Bakwalwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke’ya’ya bakwai kafin mayar da saura rami.

Balo-Balo: Wani abin wasan yara da ake sayarwa a kantuna, wanda ake hurawa iska ya kumbura.

Bangaza :(A cikin wasar  langa) Hankaɗe ko turo ɗan wasa da ƙarfi da nufin kasha shi. Misali: Musa ya ~ ƙirjin Sale.

Baran Baji: (A cikin wasar Baran Baji) 1: Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar mata. Akan yi amfani da kayan aikin gida dangin turmi da taɓarya da faifayi da makamantansu. Yana tafiya da waƙar da ke nuni da cewa, tafiya mabuɗin ilimi ce. 2: Sunan wanda ya yi shigar mata yayin wasan.

Barkwanon Tsohuwa: (A cikin wasar Yaƙi) Toka da dakakken yajin barkwano da ake haɗawa a leda domin baɗa wa abokan karawa wurin yaƙi.

Basha: (A cikin wasar Basha) 1: Wasan mata na dandali da ake gudanarwa da azumi. 2: Mutumin da masu wasan basha suka ƙudurta a rai cewa, tsoronsa ne ke hana’yan mata fitowa wasa.

Ba-taɓe Ce: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, dokar ba-taɓe za a yi amfani da ita a wasan guro.

Ba-taɓe: (A cikin wasar girjim) Dubaba-taɓe (A cikin wasar Guro).

Ba-taɓe: (A cikin wasar Guro) Dokar guro da ke tilasta mai wasa ya yi tafiya da ‘ya’yan gidan da ya taɓa da farko. Wato bai isa ya taɓa’ya’yan wani gida ba, kuma ya fasa ya yi tafiya da ‘ya’yan wani gida na daban.

Bayarwa: (A cikin wasar Langa) Kalma da ke nuna ruwa ta shirya kuma ta yarda a fara langa. Misali: Garin ruwa ne ke ~.

Belbela-Belbela: (A cikin wasar Belbela-Belbela) Wasan yarar maza ne da ke da tsarin shugabanci, wanda kuma ke da sigar salla. Bayan an gama rera waƙar wasan, kowa na ƙamewa ba tare da motsi ba.

Bena: (A cikin wasar Bena) Ɗaya daga cikin nau’ukan wasannin yara mata da ake tsanen gidaje a ƙasa sannan ake amfani da ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko wani abu mai kama da wannan a matsayin ‘yar tafiya. Akan yi tafiya ne da ƙafa ɗaya ta hanyar tsalle. Wasan yana da dokoki da dama.

Bindiga: (A cikin wasar Bindiga) Wasan yara maza inda suke amfani da ƙaramin katako ko falanki su yanke shi zuwa siffar bindiga, sannan su sanya ƙarfe mai kwararo a tsakiya su kuma ɗaure da roba. Akan yi amfani da garin kan ashana wajen ɗuri. Sannan bindigar kan ba da ƙara yayin da aka buga.

Birki: (A cikin wasar Taya) Tsumma ko igiya da ake ƙullawa jikin taya, wadda ake ja yayin da ake so ta tsaya.

Biyar Ko Goma: (A cikin wasar Biyar Ko Goma) Wasan yara maza da mata da ake amfani da ɓawon gyaɗa guda biyu. Akan dunƙule ɓawon gyaɗar cikin tafukan hannu, a kuma jijjiga, sannan a zubar ƙasa. Za a samu maki ko a faɗi, wanda ya danganta da kasancewar ɓawon gyaɗar sun buɗe gaba ɗaya, ko sun kife gaba ɗaya, ko ɗaya ta buɗe ɗaya ta kife.

Biyarwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke biyar kafin mayar da saura rami.

Biyulwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya biyu kafin mayar da saura rami.

Boka Kake Ko Malami: (A cikin wasar Boka Kake Ko Malami?) Nau’in tashe na maza manya inda ɗaya daga cikin masu wasa ke shigar malamai. Wasan na hannunka-mai-sanda kan cewa a yi hankali game da malamai da kuma malaman tsubbu.

Bori: (A cikin wasar gori/koɗi) Kalmar da ake amfani da ita don bayyana halin da koɗi take ciki na rawa da karkarwa da take yi saboda rashin zaƙi.

Bugawa: (A cikin wasar Bindiga) Matsa robar da ta riƙe wayar gareren keke domin ta bugi garin ɗuri; wanda hakan zai sa bindiga ta tashi.

Bugu: (A cikin wasar ‘Yar Cille) Doke‘yar cille da mai cilli zai yi da sanda yayin da mai kamu ya jefo ta.

Bukka Kora Ne: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, dokar guro da ake amfani da ita a lokacin da aka yi wannan furuci ya zartar cewa, duk wanda aka kai shi bukka, to daidai yake da an tatike shi.

Bukka: (A cikin wasar Guro) gida ɗaya da ya rage wa mai wasan guro.

Buƙulu: (A cikin wasar Guro) Yayin da mai wasan guro ya yi tafiya da wani gidan da bai dace ba don kawai kada abokin karawarsa ya haihu, to ya yi wa abokin karawarsa buƙulu.

Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) 1: Wasan tashe na yara mata da suke kwaikwayon tafiya da ɗabi’un manyan mata masu girman jiki. 2: Sunan da ake kiran ɓakutu a cikin wasan ɓakutu mai babban ɗuwawu.

Ɓakutu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) Jagora a cikin wasan ɓakutu mai babban ɗuwawu.

Ɓarawo Me Ka Sata: (A cikin wasar Ɓarawo Me Ka Sata) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa.

Ɓarawo: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Wanda ya yi sata yayin wasan.

Ɓata: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Lokacin da aka rasa ɗaya daga cikin ‘ya’yan wasa ko sama da haka.

Ɓata: (A cikin wasar Jini Da Jini) Yayin da mai wasa ya furta danja ga halittar da ba ta da jini, ko ya furta babu ga halittar da take da jini, to ya ɓata. Saboda haka zai fuskanci hukunci.

Ɓata: (A cikin wasar Ɓelunge) Wanda ya yi magana ba a daidai lokacin da ya dace ya yi ba, to ya ɓata wasa. Irin wannan yaro zai fuskanci hukuncin duka da rigar da aka nannaɗe.

Ɓelunge: (A cikin wasar Ɓelunge) Wasan dandali na maza da ke da sigar salla. Akan samu liman wanda zai fara gabatar da aiki, sai ladan ya yi sai kuma mamu. Wanda ya ɓata, zai fuskanci hukunci.

Ɓigo: (A cikin wasar Ɓigo) Wasan yara maza na dandali da ake gudanarwa tsakanin ɓangarorin ‘yan wasa biyu. Ya ƙunshi guje-guje da kuma duka da riga.

Ɓoyel 2: (A cikin wasar Ɓoyel 2) Wasan yara maza da mata inda akan yi tsubi-tsubi da ƙasa sannan a ɓoye tsakuwa ciki, a kuma nemi abokin wasa ya nuna cikin tsubin da aka ɓoye ƙasar.

Caccayya: (A cikin wasar Caccayya) Wasan yara maza da mata da ake gudanarwa yayin da hadari ya taso tare da alamun ruwan sama.

Cafewa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel/Carafke) Cafke ƙodo da mai wasan ‘yar carafke ke yi bayan jefa wasama.

Cafewa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Kama ‘yar wasa.

Cafkel: (A cikin wasar Carafke) Tsintar ko ɗaukar ‘ya’ya daga cikin jeri bayan an wurga ƙodo sama.

Cake: (A cikin wasar ‘yar Cake) Kafewar da abu mai tsirin da aka jefa ke yi a ƙasa.

Canji: (A cikin wasar Bena) Sauƙe ƙafar da aka ɗage tare da ɗage wadda ta ke ƙasa cikin gaggawa. Dole ne a ɗage wadda take ƙasa kafin wadda take ɗage ta taɓa ƙasa.

Canjin Gari: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Daidai da canjin gida.

Canjin Gida: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Shugabanni ne ke canjin gida, inda kowace za ta koma ɓangaren abokan wasansu.

Canjin Gida: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Juyawa ko musanyen gidaje da akan yi tsakanin masu wasa yayin da aka ƙare rakiyar-kura.

Canka: (A cikin wasar ‘yar Canka) Zaɓen hannun da ake tunanin ciki aka ɓoye tsakuwa.

Canka: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar Yata Ba) Nuna wurin da aka ɓoye ‘ya.

Cankuloto-Kuloto: (A cikin wasar Cankuloto-Kuloto) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale. Amma waƙoƙin cikinsu sun bambanta.

Carafke: (A cikin wasar Carafke) Wasan da ake jefa ƙodo sama tamkar na‘yar ramel, sai kuma a riƙa tsinar ‘ya’ya da aka yi baji da su.

Carmama: (A cikin wasar Carmama) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙa mai nuna ɗarsashin zuciya.

Carman Dudu: (A cikin wasar Carman Dudu) 1: Wasan gaɗa na dandali da ke tafiya da waƙa. 2: Sunan waƙar da ake yi a cikin wasan carman dudu.

Casana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na goma a wasan babunna.

Ci Biyu: (A cikin wasar girjim) Cin‘ya’ya biyu a tafiya ɗaya.

Ci: (A cikin wasar girjim) Tsallake ɗan abokin karawan da akwai gida a bayansa tare da ɗauke shi a matsayin wanda aka cinye.

Ci: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Sakamakon wasa, inda wanda za a ci zai haɗa tafukan hannayensa, saura kuwa su riƙa marin bayan hannuwan.

Ci: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Yayin da kura ta kama ɗaya daga cikin‘yanwasa, ta cinye ta ke nan.

Ci: (A cikin wasar Waran Warash) Duba ci (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale)

Ciki: (A cikin wasar Guro) Yayin da ‘ya’ya suka kasance guda biyu a wani gida bayan an fara tafiya, to an samu ciki a wannan gida.

Ciki: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) Tsummokara da aka tura cikin rigar Maimuna aka ɗaure ɗamar da zane domin ya tsaya a matsayin ciki.

Cilli: (A cikin wasar ‘yar Cille) Yin amfani da icen bugu domin a jefa‘yar cilli.

Cilli: (A cikin wasar ‘yar Ramel/Carafke) Jefa ƙodo sama yayin wasa.

Cilli: Tura ‘yar wasa gaba da masu wasa ke yi yayin da ta faɗo jikinta kuma suka cafe ta. Wannan na faruwa ne a wasannin yara mata da ke da tsarin cilli da direwa.

Cillo-Cillo: (A cikin wasar Cillo-Cillo) Ɗaya daga cikin wasannin dandali na yara mata inda ake amfani da kallabi ko zane ko tsumma mai ƙarfi wurin lila ‘yan wasa ɗaya bayan ɗaya.

Cin Dawo: (A cikin wasar Cin Dawo) Wasan yara mata na dandali da ake gudanarwa a zaune. Yana ƙunshe da waƙar da ke tattare da faɗakarwa.

CinFita: (A cikin wasar Gori/koɗi) Cin da ake yi wa ɗan wasan da ya nuna zai fita alhali ba a kamala wasa ba.

Cincin Sakatum: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Wasa ne na yara maza da ake gudanarwa a dandali. Yana tafiya da waƙa, wadda yayin da ta ƙare a kan ɗan wasa, to ya fita.

Ciniki: (A cikin wasar Robali) Yayin da mai kanti ya tara robali da yawa a kanti, to ya yi ciniki.

Coge: (A cikin wasar Guro) Yin tsallake ko sanya ‘ya’ya sama da ɗaya a rami guda da gangan domin neman samun nasara.

Cuwa-Cuwa: Ha’inci ko coge ko rashin gaskiya a yayin wasa.

Dabi: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Daga: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Dala: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Hukunci a matsayin sakamakon wasa. Akan bisne ‘ya’yan ‘yar ramel cikin ramin ‘yar ramel sannan wanda za a dala ta ɗora hannu bisa kai. Daga nan sauran masu wasa za su riƙa dunƙule hannu suna dukan hannun nata.

Dala: (A cikin wasar Carafke) Duka da takalmi bayan wadda ake dala ta haɗa tafukan hannuwanta, a matsayin sakamakon wasa.

Dala: (A cikin wasar Na Ɗiba) Sakamakon da ake zartarwa ga wanda tsinke ya faɗi yayin da yake ɗibar ƙasa. Za a tara ƙasa sannan ya kifa tafin hannunsa a kai. Masu dala za su riƙa dunƙule hannu suna dukan bayan hannunsa.

Dama Take Yi: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, ta dama ake yin tafiya ba hagu ba.

Damo Riya Damo: (A cikin wasar Damo Riya Damo) Wasa ne da ke da zubi da tsari irin na wasan belbela-belbela. Sai dai a wannan wasa, a maimakon a ƙame bayan an kamala waƙa, akan yi shiru ne kawai. Ma’ana, ba za a ambaci amshin waƙar ba yayin da Jagoran wasa ya rero ɗiyan ƙarshe na waƙar.

Damo: (A cikin wasar Damo Riya Damo) Furucin da masu wasa suke yi a matsayin amshin waƙar wasa. Yaron da ya yi wannan amshi bayan jagora ya rero ɗiyar waƙar ƙarshe, to ya ɓata wasa.

Danda Dokin Kara: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Wasan tashe na yara maza inda yaro guda ke hawa dokin kara lokacin tashe.

Danda: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Laƙabin da ake wa dokin karar da aka shirya lokacin wasan.

Danja: (A cikin wasar Jini Da Jini): Furucin da masu wasa ke yi yayin da aka ambaci sunan halitta mai jini, kamar akuya ko rago da sauransu.

Daƙu Fara: (A cikin wasar Daƙu Fara) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na zaune, da ke ɗauke da waƙa mai nuna muradin zuci na masu wasa musamman ta fuskar aure.

Daudu: (A cikin wasar Ga Mairama Ga Daudu) Yarinyar da take shigar maza a yayin wasan.

Digi-digi: (A cikin wasar Digi-digi) Wasan yara mata da ake yin da’ira sannan a riƙa waƙa. Wanda waƙa ta faɗa kanta, to ta fita.

Dinga-Dinga: (A cikin wasar Dinga-Dinga) Wasan tashe ne na yara mata inda suke jan hankali zuwa ga iyaye game da ɗinka wa ‘ya’yansu kayan salla.

Direwa: Faɗowa jikin masu wasa tare da dira yayin da sauran masu wasan suka cilla‘yar  wasan da ta faɗo gare su. Direwa na faruwa cikin wasannin da ke da tsarin cilli da direwa.

Dirƙe-Dirƙe: (A cikin wasar Dirƙe-Dirƙe) Wasan yara maza da aka fi gudanarwa a rafi da ke da yashi. Yara za su riƙa dira daga wuri mai ɗan tsayi zuwa cikin yashin.

Doguwar Tafiya: (A cikin wasar Girjim) Tsallake gida ko gidaje yayin tafiya. Sarki na da fawar doguwar tafiya.

Dokawa: (A cikin wasar Basha) Buga kafaɗu da masu wasa ke yi cikin ƙoƙarin ka da juna.

Doki: (A cikin wasar Dokin Kara) Karar da aka ƙuƙƙulla wa ƙyallaye da igiya (A cikin wasar linzami) a matsayin doki.

Dokin Almajire: (A cikin wasar Dokin Almajire) Wasa ne na yara maza inda wani ke sunkuyawa, wani yaron kuma ya hau bayansa. Su riƙa tafiya, tare da ɗan jagora wanda shi kuma na sunkuye zai dafa kafaɗarsa. Wasan yana tafiya da waƙa.

Dokin Kara: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Karan dawa mai ƙarfi da ake wa kwalliya da ƙyallaye domin amfani da shi yayin wasan tashe.

Dokin Kara: (A cikin wasar Dokin Kara) Wasa ne na yara maza, inda suke amfani da kararen dawa masu ƙarfi a matsayin dawaki.

Dundu: Dunƙule hannu tare da dukan mutum da hannun a bayansa.

Dundunge: (A cikin wasar Dundunge) 1: Wasan yara maza da mata inda ake rufewa ɗan wasa ɗaya ido da tsumma a kuma ba shi bulala. Duk wanda ya samu zai doka da wannan bulala. 2: Sunan wanda ake rufe wa ido cikin wasan.

Dunguren Kule: (A cikin wasar Dunguren Kule) Yawar yara maza da mata masu ƙarancin shekaru, inda suke kafa kai a ƙasa sannan su wuntsila.

Ɗage: (A cikin wasar Bena) Ɗauke ƙafa guda daga ƙasa.

Ɗagogwarogo: (A cikin wasar Ruwa Mai Malale) Amshin da ake maimaitawa yayin rera waƙar wasan.

Ɗakin Tsuntsu: (A cikin wasar Ɗakin Tsuntsu) Wasan yara maza da mata inda suke gina gidan ƙasa. Yara masu ƙarancin shekaru ne ke wannan wasa.

Ɗan Balum-balum: (A cikin wasar Ɗan Balum-balum) Wasan yara mata wadda suke layi, mai gudanar da wasa kuwa ta fito ta fuskance su. Za su riƙa waƙa tare da buɗe ƙasa da kuma tsukewa.

Ɗan Kurege: (A cikin wasar Ɗan Kurege) Wasan yara maza da mata da ke kama da wasan Na Ɗiba.

Ɗan Lele: (A cikin wasar ƊanLele) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da tsarin gidan aure. Yana nuna hoton yadda mata ke rarrashin miji da abinci iri-iri yayin da ran mijin ke ɓace.

Ɗan Maliyo-Maliyo: (A cikin wasar Ɗan Maliyo-Maliyo) Wasan gaɗa na yara mata da suke gudanarwa a dandali, wanda ke ɗauke da waƙa.

Ɗan Mutumin-Mutumin: (A cikin wasar Ɗan Mutumin-Mutumin) Tashen yara mata inda ake naɗa wa ɗaya daga cikin masu wasa tabarma a sanya hijabi a kai. Wannan yarinya za ta riƙa rawa yayin da aka je wurin wasa.

Ɗan Sanda: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Wanda ke zartar da hukuncin da sarki ya yanke wa ɓarawo yayin da ya yi sata.

ƊanTsoho Mai Cin Bashi: (A cikin wasar ƊanTsoho Mai Cin Bashi) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar tsofi sannan a goya masa matashin kai a baya. Za a riƙa dukan matashin kan tare da tuhumarsa kan ya biya kuɗin bashin da ake bin sa. Shi kuwa zai riƙa ihun neman taimakon a ba shi ya biya wannan bashi.

ƊanTsoho: (A cikin wasar ƊanTsoho Mai Cin Bashi) Sunan wanda ya yi shigar tsofi kuma aka goya masa matashin kai yayin wasan.

ƊanƁera: (A cikin wasar ƊanƁera) 1: Wasan tashe na yara maza inda suke ɗaura wa ɗaya daga cikinsu igiya a ƙugu sannan a shafe masa fuska da bula ko baƙin bayan tukunya. Yayin tashe, zai riƙa ƙoƙarin shiga wani lungu ko matsi, sauran masu wasa za su riƙa jawo shi da igiyar da aka ɗaura masa. Wasan yana ɗauke da waƙa. 2: Sunan wanda aka ɗaura wa igiya a ƙugu yayin wasan.

Ɗana: (A cikin wasar Langa) Kama ƙafa da hannu domin yin lako. Misali: Ya ~ lako.

Ɗanduƙunini: (A cikin wasar Ɗanduƙunini) 1: Wasa ne na tashe da yara maza ke gudanarwa, inda suke ɗaura wa ɗaya daga cikin su igiya a ƙugu sannan su shafe masa fuskar da baƙin tukunya ko bula. Yayin gudanar da tashen, yaron zai riƙa hanƙoron ɗaukar wani abu, amma sai a riƙa amfani da igiyar da aka ɗaura masa ana jawo shi baya. Wasan na tafiya da waƙa. 2: Sunan wanda ake ɗaura wa igiya yayin wasan.

Ɗanduƙununu: (A cikin wasar Ɗanduƙunini) Daidai da Ɗanduƙunini.

Ɗangalafe: (A cikin wasar Dokin Kara) Laƙewa ko maƙalewa a jikin doki lokacin da aka yi taɓarya.

Ɗani: (A cikin wasar Bindiga) Loja na ƙarfen garere da ake yi yadda da zarar an matsa bindiga za ta tashi.

Ɗauka: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Ɗaukar ɗa ko ‘ya’ya kafin mayar da saura rami yayin da dokar wasa ‘yar ɗaukelce.

Ɗaurawa: Lanƙwasa yatsar hannu tamkar ƙugiya tare da laƙawa a jikin na abokin wasa, sannan a ja da niyyar an yi wata yarjejeniya.

Ɗayalwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel)

Ɗayalwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ɗa ɗaya kacal kafin mayar da saura rami.

Ɗille: (A cikin wasar ‘Yar Ɗille) Yin amfani da yatsa domin feta ‘yar wasa zuwa cikin rami.

Ɗura-Ɗura: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake cilla ‘ya’yan wasa sama ana cafewa cikin salo da ƙa’ida, tare da lissafa yawan cafewa da aka yi cikin waƙa.

Ɗuri: (A cikin wasar Bindiga) Sanya garin ashana a cikin bindiga domin bugawa.

Ɗurawa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Ƙirgen da mai wasa ke yi da ke nuna tana saman abokiyar wasanta. Don haka abokiyar wasan sai ta fanshe adadin ɗura mata da aka yi ta hanyar lissafa adadin ba tare da faɗuwa ba.

Ɗuwawu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) Tsummokara ko matashin kai da ake sanya wa ɓakutu sannan a ɗaure ɗamar a matsayin ɗuwawu.

Efa-Efa: (A cikin wasar Efa-Efa) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasanWaranWarash. Sai dai a wasan ta efa-efa akan ɗauki lambobi ne.

Eskus: (A cikin wasar Sabis) Kalmar da mutum ke furtawa yayin da zai buga sabis alhali tana gidan abokan karawa. Furta wannan kalma zai sa abin da ya yi bai zama sata ba.

Fadar Sarki: (A cikin wasar ’yar Ganel) Wurin da sarki yake zaune.

Fafatawa: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Fanka: (A cikin wasar Fanka) 1: Wasan yara maza ne inda suke riƙe hannayen juna, su kuma haɗa ƙafafu wuri guda. Daga nan za su riƙa juyawa ta gefe guda (A cikin wasar hagu ko dama) tamkar dai yadda fanka ke juyawa a sama. 1: Jujjuyawa da ake yi yayin wasar fanka.

Fanshewa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Lissafin da ke nuna ana biyan bashin ɗurawar da abokiyar wasa ta yi.

Farfela: (A cikin wasar Jirgi 2) Suna ne da ake kiran wanda yake kasancewa a gaba yayin wasan.

Farin Zoben Azurfa: (A cikin wasar Farin Zoben Azurfa) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna taimakekeniya da ke wakana tsakanin abokai da kuma samari da ‘yan mata.

Fasa Ciki: (A cikin wasar Guro) Yin tafiya da ciki. Misali: A bisa tilas Musa ya ~ saboda bukka ya ke da shi.

Fasa Guro: (A cikin wasar Guro) Yayin da aka yi tafiya da guro, to an fasa guro.

Fasa Mana Guro Mu Sha Lagwada: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake faɗa wa abokin wasa musamman domin tsolaya idan ta kasance ba shi da gidan da zai iya tafiya da shi sai guro; wanda kuma idan ya fasa guron dole ne abokin wasansa ya haihu.

Fawa: (A cikin wasar Girjim) Damar da sarki ke da ita na yin doguwar tafiya ko cin ɗa daga nesa ko kasancewar ɗa ba zai iya cin sa ba ko da suna kusa.

Faɗan Layi: (A cikin wasar sabis) Ajiye sabis bisa layi tare da zaɓen mutum ɗaya daga kowane gida. Waɗanda aka zaɓa za su zo jikin layi su sunkuya, kowa daga cikin gidansa. Za a yi ƙirga daga ɗaya zuwa uku. Yayin da ake ƙirgan waɗanda aka zaɓa za su riƙa buga sandarsu ƙasa sannan suna buga sandunan a jikin na juna. Da zarar an karuku, za a rige-rigen buga sabis zuwa gidan abokan karawa.

Faɗi Mana: (A cikin wasar Faɗi Mana) Wasan yara mata na dandali da ke da zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire. A ciki mai direwa takan bayyana sunan masoyinta.

Faɗi: (A cikin wasar ’Yar Ramel/Carafke) Karya dokar wasa wanda zai sa yi ya ƙare. Wato dai, wata da ke layi ta karɓi yi.

Faɗi: (A cikin wasar Belbela-Belbela) Yayin da ɗan wasa ya yi motsi alhali an kamala rera waƙar wasa, to ya faɗi.

Faɗi: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Yayin da mai wasa ta kasa cafe ’yar wasa ko kuma ta cafe ba da hannun da ya dace ba, to ta faɗi.

Faɗuwa: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Daidai da faɗi.

Faɗuwa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Duba faɗi (A cikin wasar Ɗura-Ɗura)

Fes: Wanda zai fara wasa kafin saura.

Feshi: (A cikin wasar Bindiga) Yanayi ne da ɗuri kan fito daga cikin bindiga ya samu hannun mai bugawa.

Filin Daga: (A cikin wasar langa) Iyakar farfajiyar da aka ƙayyade wadda dole ’yan langa ba za su fita daga ciki ba yayin fafatawa.

Fita Waje: (A cikin wasar Afurka-Afurka) Fita daga cikin da’irar da ake wasa sakamakon ɓata tsarin wasa da ‘yar wasa ta yi.

Fita: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Kammala yi cikin nasara.

Fita: (A cikin wasar A Fim-Fim-Fim) Barin wasa tare da komawa gefe sakamakon ɓata tsarin wasa.

Fita: (A cikin wasar Babunna) Wadda ta gama dukan randuna to ta fita. Haka ma wadda ta kammalawan to fa yif  ta fita.

Fita: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Duk wadda waƙar wasa ta ƙare a kansa, to zai fita.

Fita: (A cikin wasar Gori/Koɗi) Daina yin wasa.

Fita: (A cikin wasar Son Makaru) Komawa gefe wanda ɗaya daga cikin’yanwasa ke yi yayin da ta tafasa uku ba tare da ɓata ba, da wadda ke gefenta na dama.

Ga Kuɗin Toshinki Na Bara: (A cikin wasar Ga Kuɗin Toshinki Na Bara) Ɗaya daga cikin wasannin tashe na mata inda suke kira zuwa ga yawaita ibada cikin watan azumi.

Ga Mairama Ga Daudu: (A cikin wasar Ga Mairama Ga Daudu) Wasan tashe na yara mata inda ɗaya ke shigar maza a matsayin Daudu. Wata daban kuma za ta kasance a matsayin matarsa, wadda kuma ke faman ba shi abinci.

Ga Zabo Zai Mutu: (A cikin wasar Ga Zabo Zai Mutu) Nau’in wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikin yara kan sa babbar rigar da ta fi ƙarfinsa. A wurin tashe wannan yaro zai kwanta ƙasa ya mai da kai da ƙafafu da hannuwa cikin rigar sannan ya riƙa shure-shure a matsayin zabo da zai mutu. Wasa ne mai tafiya da waƙa.

Gabana Gaba Nawa: (A cikin wasar Gabana Gaba Nawa) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa a zaune, wanda ke tafiya da waƙa da tafi.

Gadan Jaɓa: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke samarwa yayin wasan.

Gagarel: (A cikin wasar ‘yar Ramel) 1: Tsayawar da ɗa ke yi ya ƙi shiga rami yayin da mai wasa ta yi ƙoƙarin tura shi yayin masar babane. 2: Dama da ake ba wa mai wasa ta sake gwadawa yayin da ta faɗi a gewaya ɗan wake. Akan ba da gagarel ɗaya ko biyu ko sama da haka.

Gamuna: (A cikin wasar Gamuna) Wasan yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa. Akan gudanar da ita tsakanin ɓangarori biyu na yara.

Gardama: (A cikin wasar langa) rashin yarjejeniyar tsakanin ’yan wasa kan wani abu da ya faru yayin wasa. Wato kamar ruwa ta sha ko ba ta sha ba, ko lakon ɗan wasa ya taɓa ƙasa ko bai taɓa ba da makamantan su. misali: ’yan gidan ruwa ne suka ta da ~.

Gare: Daidai da garere

Gare-Gare: Daidai da garere.

Garere: (A cikin wasar Garere) Wasan yara maza da ke da zubi da tsari irin na wasan taya. Sai dai a wasan garere, akan yi amfani ne da garere musamman na keke a maimakon tayar mashin.

Gari: (A cikin wasar girjim) Jimillan’ya’yan mai wasa (A cikin wasar 12 ko sauran da suka rage idan an cinye wasu daga ciki) su ne ’yan garinsa.

Gari: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Ɗaya daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa.

Gari: (A cikin wasar sabis) 1: (A cikin wasar suna) ɗaya daga cikin rukunen yara da ke buga sabis tsakaninsu. Misali: Musa yana ~nmu. 2: (A cikin wasar suna) bagiren da yake ɓantaga ’yan gari ɗaya, wato daga inda layi ya fara zuwa bayansu. Misali: Musa ya yi sata a garinmu.

Gariye: (A cikin wasar Gariye) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙa. Mai waƙa takan bayyana sunan ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta.

Gewaya Ɗanwake: (A cikin wasar gori/koɗi) salon wasan gori wanda ɗan wasa ke shan abokan wasa ɗaya bayan ɗaya da zaran ya kife. Wato da zaran ya kife sai ya sha ɗaya daga cikinsu, idan ya sake kifewa kuma ya sha wani.

Gida: (A cikin wasar girjim) Kowane ɗaya daga cikin gidajen dara talatin da shida (A cikin wasar 36) da aka zana domin wasan girjim.

Gida: (A cikin wasar girjim) Zane da ake yi ko tonon gurabu talatin da shida (A cikin wasar 36), shida a tsaye, shida kuma a kwance domin zuba ’ya’yan girjim.

Gida: (A cikin wasar Guro) Kowane daga cikin ramukan da aka tona domin guro yana matsayin gida. Misali: Su Musa suna wasan guro mai ~ goma.

Gida: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Daidai da gari.

Gida: (A cikin wasar Langa) kowanne daga cikin rukunnen masu wasan langa da za su fafata da juna.

Gidaje: (A cikin wasar Bena) Zanen da ake yi a ƙasa na manyan gidajen dara, waɗanda cikinsu ake tsalle da ƙafa ɗaya yayin wasa.

Gidan Kurciya: (A cikin wasar Gidan Kurciya) 1: Wasan yara maza da mata da ake da’ira a bar tazara tsakanin juna tare da riƙe hannayen juna. Masu wasa za su riƙa shiga ta ƙasan hannayen cikin bin doka da ƙa’idar wasa. 2: Sunan tazara da ake samu tsakanin ɗan wasa da ke tsaye da kuma na gefensa.

Girgiza: (A cikin wasar Carafke) Rawa ko matsawar da ɗa ko ’ya’ya suke yi yayin da mai wasa ke faman cafkel.

Girjim: (A cikin wasar girjim) 1: Wasa dangin dara da ake zana gidajen dara talatin da shida (A cikin wasar 36) cikin layuka shida a tsaye, shida kuma a kwance. Akan yi amfani da ƙwadagon goruba da na taura ko duwatsu ko makamantansu a matsayin ’ya’ya. 2: Furucin da mai wasar girmin kan yi yayin da zai yi tafiya, musamman domin zolayar abokin karawarsa cewa zai cinye shi.

Gociya: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Zamewa da wanda ake ci zai yi yayin da aka kawo duka da niyyar ci.

Gociya: (A cikin wasar Waran Warash) Duba gociya (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale).

Goga: (A cikin wasar goga) 1: (A cikin wasar suna) wasan da ake rami a jikin gaɓar kara domin a samu dammar lanƙayawa a jikin gaɓar karan abokin wasa, sannan a ja har sai kan gaɓar karar ɗaya daga cikin’yan wasa ya ɓalle. 2: (A cikin wasar suna) Gaɓar karan da aka yi ta wasan goga da ita ba ta karye ba. Misali: Wa zai ja da ~ ta?

Gomalwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta mayar ɗa ’ya’ya cikin rami ɗaya bayan ɗaya. Shi ne matakin ƙarshe na kowace randa.

Gomanna: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na biyu a wasan babunna.

Gora-Gora: (A cikin wasar Gora-Gora) Wasan gaɗa ne na mata da ake gudanarwa a dandali, wanda kuma ke ɗauke da waƙa.

Gori: (A cikin wasar Godi/koɗi) 1: (A cikin wasar suna) suna da ake kiran wasan gori da shi. Daidai da koɗi. 2: (A cikin wasar suna) ƙoƙon dodon koɗi da aka gyara, ko marfin biro da aka sanya wa fayafayen babban batirin rediyo domin yin gori da shi. 3: (A cikin wasar aikatau) jujjuyawa ko wainuwa da gori ke yi yayin da aka gara ta.

Goron: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Goruba: (A cikin wasar Waran Warash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Goɗiyallare: (A cikin wasar Goɗiyallare) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙar da ta ƙunshi baƙar magana ga uwar miji.

Goye-Goye: (A cikin wasar Goye-Goye) Wasan yara mata ne inda ɗaya daga cikin masu wasa za ta goyi ‘yaruwarta ta yi tafiya da ita zuwa wani ƙayyadadden wuri. Yayin da ta gama, ita ma za ta rama mata. Wato za ta goye ta yi daidai wannan tafiya da ita.

Goyo: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) ’Yar tsana da Maimuna ke goya yayin wasa.

Goyon Baya: (A cikin wasar Goyon Baya) Wani nau’i ne na wasan goye-goye inda mai goyo da wanda aka goya ke haɗa bayansu.

Goyon Kura: (A cikin wasar Goyon Kura) Wani nau’i ne na wasan goye-goyen inda wanda aka goya ke kasancewa a ranga-ranga kan bayan mai goyo.

Gula: (A cikin wasar Langa) Yayin da ɗan wasa ya harbi abokin karawarsa da dunduniyar ƙafar da ya yi lako da ita, to ya masa ƙulli. Wannan laifi ne a dokar langa.

Gulum-Babu: (A cikin wasar Noti-Noti) Furucin da ake yi wanda ke nuna cewa, abin da aka ambata ba ya ɗauke da noti.

Gulum-Noti: (A cikin wasar Noti-Noti) Furucin da ake yi wadda ke nuna cewa, abin da aka ambata yana ɗauke da noti.

Guro: (A cikin wasar Guro) 1: (A cikin wasar suna) wasa dangin dara da ake amfani da duwatsu ko ‘ya’yan kanya ko makamantansu. Akan toni ramuka goma sha biyu sannan a sanya uku-uku a kowanne rami. Wani lokaci akan kira ta da ‘yar guro. 2: (A cikin wasar suna) ‘ya’ya uku na ƙarshe da ake ba wa wanda ya yi tafiya bayan an kamala tafiya. Misali: Musa ne ya yi tafiya yanzu, saboda haka  shi za a ba wa ~. 3: Gidan da aka yi ta tafiya ba tare da an kwashe shi ba. Saboda haka ‘ya’yan gidan sun yi yawa sosai.

Gwabzawa: (A cikin wasar langa) fafatawar da ake yi yayin da ruwa ta bayar har zuwa ruwa ta sha ko a kashe ta ko a yi jaga ko zubel. Misali: Ruwa ta tsinke ta sha a yayin da ake ta ~.

Gwanjo-Gwanjo: (A cikin wasar Gwanjo-Gwanjo) Wasan yara maza da suke haɗa rigunansu wuri guda sannan su jefa sama. Za a yi wawan cafewa tun suna sama. Duk wanda ya cafe rigarsa, zai nannaɗa ta daɗin duka. Za a rufe na ƙarshe da bai ɗauki irgarsa ba da duka har saiya je ya sha.

Gwauro: (A cikin wasar Gwauro) 1: Wasan tashe na manya maza inda sarkin gwauro ke kama gwagware. 2: Sunayen waɗanda sarkin gwauro ke kamawa sakamakon ba su da aure.

Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake rabuwa gida biyu kafin fara ta. Yana tafiya da tsarin shugabanci. Akan rufe wa ɗaya daga cikin masu wasa ido, sannan wata daga ɓangaren abokan karawa ta zo ta bugi kanta ta koma ta zauna cikin