Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Martaba Walin Zazzau Ummaru Ɗan Sarkin Zazzau Ɗalhatu

 Walin Zazzau Ummaru Ɗan Sarkin Zazzau Ɗalhatu
"Baban Shamaki na Wali Ummaru Ɗan Sanda ba maza tsoro" cewar Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Narambaɗa Tuubali a Waƙarsa mai amshi ' Mijin Nana Yalwa Ɗan Sanda, gulbi kawuce kwalhewa' wadda ya yi wa Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Muhammadu Aminu (yayi sarauta daga shekarar 1959 zuwa rasuwarsa a shekarar 1975). Wannan shi ne Walin Zazzau Ummaru Ɗan Sarkin Zazzau Ɗalhatu, ya yi sarautar Walin Zazzau daga shekarun 1920s zuwa rasuwarsa a shekarar 1984, ya kuma zauni gundumomin Lere da Ikara a matsayin Hakimi. Shi ne wanda Makaɗa Narambaɗa ke nufi a cikin wannan ɗan Waƙar kuma mahaifin Walin Zazzau na yanzu, Engineer Aminu Umar. Allah ya jiƙan magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Daga Taskar

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815

Post a Comment

0 Comments