Ticker

6/recent/ticker-posts

Babi Na Biyar - Shimfida

5.0 Shimfiɗa

Wasannin yara maza sun bambanta da da na yara mata ta fuskar zubi da tsari. Wasannin yara maza sukan bukaci amfani da ƙarfi sama da na yara mata. Sannan an fi samun kasada da ƙiriniya a cikin wasannin yara maza sama da na yara mata. Kasancewar an kawo rabe-raben wasanni a babukan da suka gabata, a wannan babi an kawo bayani ne kan wasu wasannin yara maza kamar dai yadda ake gudanar da su a ƙasar Hausa. Ma’ana, an kawo su ne zube, ba tare da rabe tsakanin rukunoninsu ba (misali na tashe da na dandali da makamantansu). An yi hakan bisa niyya, kasancewar duk wani bayani da za a buƙata dangane da rabe-raben wasanni an kawo shi a babi na biyu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments