Ina Yawan Tunani A Cikin Sallah, Yaya Zan Yi?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum Malam da fatan kana lafiya, tambayata Anan ita ce nakasance ina yawan tunani a cikin sallah, menene mafita? Nagode

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله

    Yawan tunani a cikin sallah ko aduk wani aiki na ibada da mutum yake aikatawa yana daka cikin aikin Shaiɗan wanda yake cutar da bayin Allah muminai dashi, har sai yasanyawa mutum damuwa dakunci darashin nutsuwa dangane da aikinda yagabatar, shi ne ya saka masa damuwa dangane aikinda yake aikatawa, sai aikin ya zamarwa mutum wahala da bakin ciki da danuwa, maimakon ya zamto masa kwanciyar hankali da nustuwa da hutu da azuciyarsa.

    Maganin yawan tunani asallah yana cikin abubuwa biyu masu sauki, sune: riko da ambaton Allah, da kau da kai daka yawan tunanin, dazarar tunanin yazowa mutum asallar sa ya kau dashi daka zuciyarsa, ya saka mata tunanin wani abun na lahira, maganin dai shi ne dauke zuciya daka tunanin dayazo masa asallarsa zuwa wani abun daban.

    Kada mutum yadamu da abun da yake zuwar masa narashin cikar tsarkinsa ko alwalarsa ko cewa anya ban yi tusa ba ko anya awajan tsarki fitsari bai tabamun tufafi ba, ko bai fallatsarminba, ko bayan nagama tsarki ragowar fitsarin bai digo min ba, duk lokacin da mutum yaji wannan ya yi wurgi dashi, shi ne yadaukeshi bai faruba bashida yakini, bai faruba kawai yaci gaba da sallarsa.

    Annabi sallallahu Alaihi wasallam yashiryar damu akan wanda yawan tunani yake zuwar masa asallarsa ya ce: (yanemi tsarin Allah daka Shaidan yabar tunanin ) bukhari (3276) da muslim (134).

    Amma biyewa tunanin dacigaba dayinsa, wannan yana jefa mutum cikin damuwa da takura dabakin ciki, kuma zai iya kai mutum ga hauka, yafitar dashi daka jerin masu hankali.

    Asar ya zo daka Ai'isha Allah yakara yarda da ita ta ce: (Wanda aka jarraba dayawan tunani ya ce: mun yi imani da Allah da manzansa sau uku, wannan tunanin zaitafi daka gareshi).

    Yazo a cikin sahihu muslim daka usman bin Abil Ãaas yace : Shaiɗan yana rikitani tsakanina da sallah ta da karatuna, sai Annabi salallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Wannan wani Shaiɗan ne da'ake ce masa kanzab, kanemi tsarin Allah dashi ka yi tofi abangaren hagunka sau uku,) ya ce: sai nayi haka sai Allah yatafiyarmin dashi,.

    Imamun nawawi rahimahullah ya ce: wasu malamai sukace: an so wanda tunani ya zo masa asallah ko alwala ko tsarki ya ce: La'ilaha illallahu, domin Shaiɗan idan yaji an ambaci Allah yana dakatawa baya iya karasowa wurin, la'ilaha ilallahu kuma ita ce tushen duk wani ambaton Allah.

    Mafi amfani wajan magance matsalar tunani asallah shi ne yawaita ambaton Allah, Fatawa fiƙhiyyah Alkubra (1/149).

    Maganin yawan tunani asallah shi ne yawaita ambaton Allah, dakuma rokonsa waraka akan hakan, darashin mika wuya ga tunanin, wajibi ne mutum yakauda tunanin duk sanda ya zo masa, kamar ka yi tsarkin fitsari ko wankan janaba, sai tunani yafado maka cewa baka wanke kankaba to kada kaci gaba da tunanin baka wanke kankaba, kawai zaka sawa ranka karyane kawanke kanka, kawatsar da tunanin gaba daya haka za ka yi asauran ibadoji, zakana watsar da duk wani tunanin dayazo maka, kada kaci gaba dayinsa, domin daka Shaiɗan ne, kayawaita neman tsarin Shaiɗan wajan Allah.

    Fatawa lajnatul da'imah (5/226)

    Koda asallah ne idan tunani ya zo maka ka yi kayi wajan wurgar dashi amma yana dawo maka, yahalatta kai a'uziyya ka yi tofi a ɓarin hannun hagu dinka sau uku.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.