𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahamatullah,
malam dan Allah mutum ne ya yi umarah a watan shawwal to yanzu in mutum zai yi
aikin Hajj Tumatu'i Sai ya sake wani umarah? Allah ya ba da ikon amsawa.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu Wa
Rahmatullah, ‘yar uwa dama shi aikin Hajji na Tamattu'i malamai sun bayyana shi
da cewa: Shi ne mutum ya yi aikin Umra a cikin watannin aikin Hajji, daga bisa
kuma sai ya dawo ya yi aikin Hajji.
Watan Shauwal yana daga cikin
watannin aikin Hajji kamar yadda maz'habobi huɗu na Fiƙhu suka tabbar. Tun da
haka ne to ashe ba sai kin sake yin wata umra ba, tun da dama Hajjin Tamattu'i
shi ne maninyaci ya yi umra a watannin aikin Hajji, daga bisani kuma ya zo ya
yi aikin Hajji.
Watanin Aikin Hajji su ne
Shauwal, da Zhulƙa'ada, da kuma Zhulhijja gaba ɗayansa a Maz'habar Malikiyya.
Amma a maz'habar Hanafiyya, da Hanabila, watannin aikin Hajji su ne Shauwal, da
Zhulƙa'ada da kuma kwanaki goma na farkon Zhulhijja.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.