Ticker

6/recent/ticker-posts

A Kan Wa Aure Ya Wajaba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malam ina son na san suwaye aure yawajaba a kansu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Hukunci Aure yana Sabawa da saɓanin halin da Mutum ya Samu kansa da Kuma Abun da yake dashi, Aure wajibi ne akan Wanda ya Samu iko, Idan ransa yana so kuma yana tsoran Aukawa zina, domin tsare kai, da Kame kai daka haram dolene, hakan ba zai Samu ba saida Aure.

Ƙurduby ya ce: Wanda yake da damar Aure yake tsoran cutar da kansa da Addininsa daka sha'awar da bata gushewa saida Aure, Babu Wani saɓani akan Wajabcin Aure a kansa.

Marudi Rahimahullahu a cikin littafinsa Al-Insaaf ya ce: Wanda yake tsoran fadawa zina, Aure a kansa Wajibi ne kai tsaye, .

Duba Al-Insaaf Mujalladi na (8) Kitabul Nikah, Ahkamul Nikah.

Idan ransa yana Son Aure, amma yasan ba zai iya ciyar da matar ba, sai ya kame.

Fadin Allah madaukakin sarki ya wadatar Masa (Waɗanda Basu samu halin yin Aure ba, su kame har sai Allah ya wadatasu daka falalarsa...

Ya kuma ya waita Azumi, domin azumi kariya ne daka Sha'awa.

Kamar yanda Abdullahi dan Mas'uud ya ruwaito daka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam.

Duba Fiƙhussunnah (2/15-18).

Wajabcin Aure baya faduwa akan Wanda yasan ba zai iya haƙura da Saɓawa Allah ko fadawa zina ba ko kallace kallace da Sauran Abubuwa da Shari'a ta tsoratar..

Duk Wanda ya yi nazarin Wannan zamanin da Muke ciki da Abun da yake tattare dashi na ayyukan ɓarna kala-kala, zai gamsu cewa wajabcin yafi tsanani da Ƙarfi sama da Za munnan da Suka wuce..

Muna Roƙon Allah ya tsarkake zuƙatanmu ya Nisantar da tsakaninmu da Haram, ya Azurtamu da Kamewa.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments